Kanwan Katsina Yayi Kira Ga Al’umma Dasu Bada Goyon Doncin Nasarar Aikin Rigakafin Cutar Shan Inna.
Kanwan Katsina, Hakimin Ketare dake karamar hukumar Kankara, Alhaji Bello Usman Kankara, ya yi kira ga al’ummomin da ke gundumar ta Ketare da su ci gaba da ba da cikakken goyon baya da hadin kai a bangarorin rigakafin cutar shan inna.
Yayi wannan kiran ne a wata ganawa da yayi da duk shugabannin kauyukan a fadarsa dake Ketare.
Ganawar ta biyo bayan taron da Hakimin ya yi a baya tare da mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji AbdulMumini Kabir Usman tare da jami’an Hukumar kiwon Lafiya a matakin ta Jiha wadanda suka je fadar don neman shawarwari.
Ya kuma sanar da shugabannin kauyukan cewa nan ba da dadewa ba, jami’an hukumar kiwon lafiya za su fara yin rigakafin cutar shan inna da sauran cututtukan da suka dace.
Basaraken ya jaddada bukatar mutanen yankin nasa su ci gaba da daukar matakan kariya kan Covid-19 wadanda suka hada da yawaita wanke hannu, sanya takun kumin fuska, amfani da kayan goge hannu da kuma guje wa manyan taruka.
Ya kuma umarci dukkan shugabannin addinai a gundumar da su ci gaba da sanya sakonnin rigakafi a cikin wa’azinsu da Hudobinsu a lokacin sallar Juma’a da salloli biyar na kowace rana


































