Gwamnatin Kaduna da ke arewacin Najeriya ta umarci makarantun jihar da su tabbatar sun kammala jarrabawa sun rufe zuwa ranar Laraba, 16 ga watan Disamban 2020.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ƙaruwar yaɗuwar korona a jihar da ma ƙasar baki ɗaya.
A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar wadda ke ɗauke da sa hannun kwamishinan ilimi na jihar, za a dakatar da koyar da karatu a cikin aji a makarantun sakandare da jami’o’i da kwalejoji da ke jihar inda aka buƙaci makarantun su nemi wasu hanyoyi na koyarwa da suka haɗa da ta intanet.
Gwamnatin jihar ta kuma ce za a ci gaba da koyarwa ta gidan talabijin da rediyo na jihar kamar yadda aka rinƙa yi a lokacin kullen korona a baya.