A cikin wani faifain bidiyo da kungiyar ta fitar, an ji Shugaban Ƙungiyar Abubakar Shekau na bayyana cewar Ƙungiyar su ta Boko Haram ita ce ta sace ɗaruruwan ɗalibai dake Makarantar sakandaren Kimiyya dake ƙaramar Hukumar Ƙanƙara a ƙarshen Mako.
Shekau ya kara da cewar babban maƙusudin sace ɗaliban shine domin nuna kyamata da karatun Boko a yankin, kamar yadda ya bayyana karatun Boko a matsayin kafirci kuma dole a tsarkake kasar Najeriya daga kafirci.
Kalaman nan Shekau dai na zuwa ne a daidai lokacin da tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a yankin Arewacin Najeriya, kuma hasashen da jama’a ke yi na haduwar Boko Haram da ‘yan Bindigar Arewa maso yamma ya nuna da alamun gaskiya kenan.
Sama da dalibai 600 ne ‘yan Bindigar suka sace a ƙarshen mako a makarantar Sakandaren Kimiyya da ke ƙanƙara, aka shiga cikin kungurmin daji da su, wanda har ya zuwa yanzu da dama daga cikin su suna hannun ‘yan Bindigar.
Sai dai a wani labari na daban Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana cewar 16 daga cikin daliban sun samu kubuta, kuma ana cigaba da tattaunawa da ‘yan Bindigar domin ganin an sako sauran daliban.