Tsohon ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya majalisar Dattawa Kwamared Shehu Sani, ya ce dole ayi tir da masu ta’addanci da rigar musulunci a kasar Faransa, sai dai wannan bai hana shi yin tir da aikin Shugaba Macron ba.
Ɗan siyasar ya ce babu abin da zai hana a fito a yi tir da abin da shugaban kasar Faransar ya yi na ba masu yi wa addinin musulunci isgilanci goyon-baya.
“Ya kai @EmmanuelMacron, dole ayi tir da duk wani harin ta’addanci ko zagon-kasa da aka yi a kasar Faransa da sunan musulunci, tsantsar hauka ce da tsantsangwaron rashin imani.”
Dear @EmmanuelMacron,any terrorists attacks or sabotage committed in France in the name of Islam is sheer madness and cruel evil that stands condemned.Your direct & implied support for actions that denigrated Muslims & desecrated Prophet Muhammad PBUH stands equally condemned.
— Senator Shehu Sani (@ShehuSani) October 26, 2020
“Mara baya kai-tsaye ko a kaikaice da ka ke yi ga masu bata musulunci ko cin mutuncin Annabi Muhammad (tsira da aminci a gareshi), duk shi ma abin ayi Allah-wadai ne.”
Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya majalisar dattawa tsakanin 2015 zuwa 2019, ya yi wannan magana ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.