Za A Daina Zubar Da Jinin ‘Yan Arewa A Mulkin Buhari Kuwa?
A hirar da ya yi da manema labarai a Kaduna, Alhaji Nastura Ashir Sherif ya bayyana irin halin da jama’ar Arewa suka tsinci kansu na kisan da ake yi musu yanzu haka a sashin Kudancin Najeriya musamman Jihohin Yarabawa.
Shugaban gamayyar Kungiyoyin Arewan, Ashir Sherif ya ce ko kadan wannan gwamnati ba ta dauki rayuwar dan Arewa a bakin komai ba, abin da kawai aka dauki dan Arewa shi ne gugar yasa wanda amfanin sa kawai ya fito lokacin zabe ya jefa kuri’a, a haye madafun iko a bar shi a rana.
Ya kuma bada misali da kokarin da sanannen malamin nan Dr. Ahmad Gumi ke yi na ganin an shawo kan matsalar tsaro a yankin Arewa, amma abin mamaki da takaici maimakon a yaba mishi ko a goya mishi baya, sai ya zamana an fito ana ta sukar shi.
“Kowa ya ga irin cin zarafin da shugaban tsagerun Yarbawa Sunday Igboho ke yi, na jagorantar Zanga-Zangar kisan ‘yan Arewa a Kudu ba tare da samun wata turjiya ba, amma a lokacin da Matasa a Arewa suka shirya gudanar da Zanga-Zanga ta Lumana akan jan hankalin Gwamnati na tabarbarewar tsaro a Arewa, nan take jami’an tsaro suka dakile shirin, sannan aka yi amfani da Malaman Addini suka hau mimbari suna fafin wai babu Zanga-Zanga a cikin Addini”.
Nastura Ashir Sherif ya bayyana cewar dan Arewa ya sani kuma ya daina yaudarar kan shi wannan gwamnati ta Buhari ba ta da wani shiri na kare rayuwar shi, kuma lallai ne rayuwar dan Arewa na cikin hatsari a wannan gwamnatin, domin wadanda suke rike da ragamar tsaro a kasar duk da kasancewar su ‘yan Arewa ba Arewa ce a gaban su ba.