Wani bincike a Jamhuriyar Chadi ya gano cewa fursunonin da suka mutu a farkon wannan shekara saboda mummunan yanayi a cibiyar da ake tsare da su, ba guba aka ba su ba.
Hukumomi tun da farko sun nunar cewa mai yiwuwa ne guba ce ta yi sanadin mutuwar ɗaurarrun.
A watan Afrilun bana ne aka gano gawawwakin mutanen cikin wani gidan yari.
Suna cikin mutum 58 da aka kama bisa zargin kasancewarsu ‘ya’yan ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi.
Binciken na wata hukuma mai zaman kanta ya gano cewa mutanen sun mutu ne saboda zafi da ƙishirwa da yunwa a sansanonin da aka tsare su mai matuƙar cunkoso.
Hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Chadi ta ce babu wanda ya kai wa ɗaurarru wani ɗauki duk da yake sun shafe tsawon daren ranar suna neman agaji.
Hukumar ta kuma ce an tsare su da daɗewa bayan sojoji sun gudanar da wani aikin fatattakar ‘yan Boko Haram, inda ta kuma nuna cewa mutanen sam ba ma ‘ya’yan ƙungiyar ba ne.
Tasirin wannan rahoton shi ne rundunar sojojin Chadi na aikata laifin amfani da hanyoyin ƙeta irin waɗanda takwarorinsu a Najeriya ke amfani da su.
Aika-aikar da sojoji suka tafka da kuma kamen mutane ba ji ba gani sun fusata rayukan al’ummar yankunan da ke fama da rikici, abin da kuma ya sanya yaƙi da masu iƙirarin jihadin ƙara zama mai wahala.