A jiya Lahadi ne shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya nuna damuwarsa a kan yawan mace-macen da ke faruwa a jihar Yobe.
A wata takarda da mai magana da yawun Lawan, Ola Awoniyi ya fitar, ya yi kira ga yankunan da su bai wa hukumomi a jihar hadin kai don binciko abinda ke kawo mace-macen.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, Lawan ya ce, “Kokarin da gwamnati ke yi a yanzu shine bincike a kan mace-macen.
Mutuwar kamar kowacce iri ce ko kuma akwai cutar da ke kawo ta. Ta hakan ne kadai za a iya shawo kan matsalar.
Yawan mace-mace a Yobe – Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa kan abunda ke wakana a mahaifarsa
Ahmad Ibrahim Lawan yace “Dole ne a tallafawa gwamnatin jihar a yanzu don samun sakamakon da ya dace.
Suma jamaar Yankunan ana bukata su bada hadin kai don bai wa hukumomi damar nasarar bincike.”
Ya jajanta da iyalai da abokan arzikin mamatan tare da musu fatan rahama.