A yayin da ake ci gaba da fama da annobar korona a duniya, yau Talata ce ranar ma’aikatan jinya ta duniya.
Wannan ranar ce kuma ranar da ake tuna wa da cika shekaru 200 da haifar Florence Nightingale- wata ma’aikaciyar Jinya ‘yar Burtaniya da ta taimaka wa sojoji a lokacin yakin Crimea.
Kungiyoyin da ke wakiltar ma’aikatan Jinya sun nuna damuwarsu kan yadda ake musu a wannan lokaci da duniya ke fama da annoba har a kasashen da ake gani suna da arziki.
Sun ce akwai gazawa wajen gwaje-gwaje a asibitoci da karancin kayayyakin kariya wato PPE, da kuma rashin tallafa musu a bangaren lafiyar kwakwalwa saboda damuwar da suke shiga, ganin sune a gaba-gaba a wannan yakin.
Kungiyar ma’aikatan jinya ta duniya ta yi gargadi cewa suna cikin hadarin karar da ma’aikatansu a lokacin da duniyar tafi bukatarsu.