Yariman Saudiyya Turki Al-Faisal bin Abdulziz al-Saud, kuma tsohon shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar ya caccaki Isra’ila inda ya kira ta babbar mai mulkin mallaka da ke amfani da ƙarfi da rusa matsugunin Falasɗinawa.
Yarima Turki al Faisal ya yi waɗannan kalaman ne a wani taron tsaro ta intanet da Bahrain ke jagoranta a Manama a ranar Lahadi wanda ya samu halartar ministan harakokin wajen Isra’ila Gabi Ashkenazi wanda ya yi watsi da kalaman.
Al-Faisal ya ƙara da cewa “Isra’ila tana rusa gidaje yadda ta ga dama kuma tana kashe duk wanda take so.”
Amma a martaninsa, ministan harakokin wajen Isra’ila ya ce ya tausayawa kalaman da suka fito daga yariman.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa “zargin karya da jami’in Saudiyya ya yi a taron Manama ba ya nuna gaskiya ko asalin canjin da yankin ke ciki.”