Yan kasuwa a jihar Kano sun bullo da sabuwar hanyar sayar da hajojinsu duk da dokar kulle da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar ya saka domin dakile yaduwar annobar COVID-19
Yan kasuwan, galibsu daga kasuwar Kantin Kwari da Kofar Wambai sun koma unguwanni a Fagge inda suka baje kolinsu kuma babu bayar da tazara tsakaninsu.
A ranar 2 ga watan Mayu ne Gwamna Ganduje ya sassauta dokar kullen inda ya bawa wasu kasuwanni ikon buduwa a ranakun Litinin da Alhamis don mutane su saya kayan azumi.
Korona: ‘Yan kasuwan Kano sun koma sayar da kayayyaki a unguwanni saboda dokar kulle.
Hoto daga Premium Times Source: UGC Gwamnan ya ce za a rika zirga zirga ne daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma a ranakun walwalar kuma masu sayar da nama da masu sayar da kayan gwari aka bawa damar bude shaguna.
[covid-data]