Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta fitar da tsarin yadda matafiya za su sayi tikitin jirgin ƙasa ta intanet.
A yanzu dai matafiya da za su yi tafiya daga Kaduna-Abuja ko kuma daga Abuja-Kaduna a jirgin ƙasa za su iya siyan tikitin su daga gida ba tare da bin layi a tashar jirgi ba.
Tun a baya, jama’a da dama masu bin jirgin sun sha ƙorafi ga gwamnatin ƙasar da ta fito da tsarin da zai sauƙaƙa siyan tikitin jirgin, inda akasari suka bayar da shawara a koma sayar da shi ta intanet.
Hakan ya biyo bayan zargin cin hanci da rashawa da ya dabaibaye tsarin siyar da tikitin a duka tashoshin Abuja da Kaduna.
Ga yadda za ku bi domin sayen tikitin
- Za ku iya shiga www.nrc.tps.ng domin shiga shafin intanet na hukumar ko kuma ga masu android, su je Google Play Store domin sauke manhajar NRC E-ticketing App
- Idan kuka shiga shafin, za ku ga wurin zaɓen tashar da mutum zai tashi da tashar da mutum zai sauka. Misali, mutum zai iya zaɓen ya tashi daga Rigasa zuwa Kubwa ko kuma Idu zuwa Rigasa.
- Bayan nan sai mutum ya zaɓi ranar da yake so ya yi tafiya, sai ya latsa “Find my train”, wato mutum zai nemi jirgin da yake so.
- Daga nan, manhajar za ta kai mutum wani shafi na musamman da zai sa sunan da ya yi rajista da kuma lambobin sirrinsa (password), ga kuma wanda bai yi rajista ba abu mai sauƙi ne, domin akwai wurin da za a latsa ya yi rajista.
- Idan aka latsa “signup”, za a kai mutum wani shafi da zai saka adreshinsa na email da sunansa da password da lambar waya da ranar haihuwa. Haka kuma akwai zaɓin mutum ya saka lambarsa ta NIN ko kuma amfani da katin zaɓe.
- Da zarar mutum ya kammala rajistarsa zai iya komawa wurin farko da ya fara sayen tikitin domin ya ci gaba.
- Za a ba mutum damar zaɓar jirgin da yake so da taragon da yake so da kuma lambar kujera.
- Daga nan kuma mutum zai je shafin da zai yi amfani da katinsa na atm domin biyan kuɗin jirgi