Dattijo Alhaji Ado, wanda ‘yan bindiga suka sace da jikokinsa guda biyu da ke garin Dodo, a yammacin garin Wagini da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, ya bayyana irin ukubar da ‘yan bindigar da suka sace su kwanaki goma sha ukku tare da mutanen garin su, talatin da biyar maza da mata, suka kora mu daji kamar awaki ba takalma a kasa mu ka yi ta tafiya har muka isa maboyar su.
Alhaji Ado ya bayyana irin rayuwar da suka yi a tsawon wadannan kwanakin a hannun su, a lokacin da aka kubutar da su aka kawo su gidan gwamnatin jihar Katsina.
Alhaji Ado, wanda dattijo ne mai mata ukku kuma manomi ya ce “yau kwanan mu goma sha ukku a hannun yan bindiga, da safe suna ba mu danyen dankali da rana kunu. Mu talatin da biyar ne suka dauka kuma waje daya muke kwana, cikin wata bukka. Kuma suna bugu, har rauni suka ji man kusa da ido, har sai da idona ya kunbure, kuma a kasa muke kwana. Wadannan yara guda biyu ‘yayana ne.Tunda muka je ba mu ga wulgin jami’an tsaro, amma idan jirgi ya wulga suna boyewa. Yau da safe suka ce mana mu fito, mu tafi gwamnati ta karbe mu, suka kawo mu bakin daji sai muka ga motoci da jami’an tsaro muka hau aka kawo mu nan.
Daga karshe muna mika godiya ga gwamnati jihar Katsina, karkashin gwamna Aminu Bello Masari, mun ji dadi kwarai da aka kubutar da mu kuma ba su kashe kowa ba.