Ya kamata gwamnati ta Maida hankali A Harkar Tsaro fiyeda Corona – Sanata Abu Ibrahim
Sanata Abu Ibrahim, ya ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar siyasa cikin shekara 21 data shafe karkashin mulkin farar hula.
Sanatan wanda ya bayyana haka dai-dai lokacin da ake bikin ranar dimokradiyyar kasar ya fada wa BBC dalilian da ya sa yake ganin a siyasance Najeriya ta ci gaba.
Ya bayyana cewa a baya an fuskanci tarin kalubale musamman lokutan zabe amma samar da na’urar tantance katin zabe ta taimaka wajen rage yawan satar kuri’u da yin amfani da “bindiga da adduna”.
Akwai jituwa tsakanin bangaren gwamnati dana ‘yan majalisa dana masu shari’a.” kamar yadda Sanata Ibrahim ya bayyana.
A cewarsa, “Dimokradiyya ta samu gindin zama” saboda zai yi wuya a iya sake kwace mulkin Najeriya”.
Ta fuskar tsaro kuma, dan siyasar ya ce an samu galaba kan Boko Haram sannan an kawo wani sabon canji wanda ya bai wa ‘yan sanda damar samun kudade akai-akai wanda doka ta basu.
“Babbar matsala a yanzu gaskiya wanda dole sai an tashi tsaye shi ne maganar kashe-kashe da ake yi a arewa maso yamma – Katsina da Zamfara da Kaduna da (wasu bangaren Neja da Sokoto),”
“A ganina dole gwamnati ta tashi kamar yadda ta tashi kan (cutar korona) wadannan ‘yan ta’adda dole a yake su tun da ai suna kashe mutane bayin Allah.”
Ya nemi gwamnati ta samar da kwamiti da zai yaki ‘yan ta’addan wanda ya ce “Ba kallonsu za a yi ba, dole a yake su.”
Sanatan ya kara da cewa ya kamata kwamitin ya nada wani gwamna a matsayin shugaba sannan a sa ministan tsaro da babban sifeton ‘yan sanda da ministan cikin gida da sauran gwamnoni a matsayin mambobin kwamitin.
Ya ce bai wa kwamitin wa’adin wata daya ya gudanar da bincike kan hare-haren zai samar da mafita ga lamarin.
Sanata Abu Ibrahim, ya kara da cewa kamata ya yi a samu hadin kai tsakanin yankunan da ke fama da wannan matsala ta rashin tsaro domin samar da mafit