Wata Budurwa data haihu tace ta iska cikin ya shigeta
Wata Budurwa data haihu ta yi ikirarin cewa ta Iska cikin ya shiga jikinta. Wani katin abin ban mamaki shine, tace kawai bayan da ta ji iskan ya shiga jikinta, Sai ta ji cikinta na kumbura, Bayan Awa 1, Kawai sai ta Haihu.
‘Yansanda sun fara Bincike a kasar Indonesia bayan da Sti Zaina ‘yar shekaru 25 ta yi wannan ikirari.
Lamarin ya farune a Cianjur dage West Java na kasar. Tace bayan Sallar Azahar, tana kwance kawai sai iska ya shiga jikinta, Mintuna 15 bayan nan sai cikinta ya fara kumbura yana mata ciwo.
Tace nan aka garzaya da ita Asibiti inda ta haifi diyarta.
Shugaban yankin, Eman Sulaiman ya tabbatar da faruwar Lamarin inda yace amma suna Tunanin tana dauke da cikinne bata sani ba sai lokacin Nakuda.