Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Nigeria, Sheikh Dakta Ahmed Gumi shima ya fitar da fatawar cewa duk dan wasan kwaikwayo da ya saki matarsa a cikin shirin fim to matansa na gida sun saku.
Manuniya ta ruwaito Dakta Ahmed ya amsa tambayar da wani yayi masa a yayin zaman karatun Fighu na mako-mako da yake yi a masallacin Sultan Bello zama na 57, ya ce ko shakka babu matansa na gida sun saku sai dai idan ya fayyace a yayin da yake yin sakin ko da a fim din ne.
Idan yana da mata sama da daya sai yace ya saki matarsa kuma bai fayyace wa yake nufi ba (misali yayi ishara ga wannan yar fim da ba matarsa bace) to duka matansa na gida sun saku inji Dakta Ahmed Gumi