Shugaba Muhammadu Buhari ya hana Ministoci tsige Shugabannin Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.
A yanzu an shigo wa wani tsari, wanda ya kara wa Sakataren Gwamnatin Tarayya karfin iko a sha’anin hukuntawa ko tsige shuganan wata ma’aikata ko hukumar Gwamnatin Tarayya da ke karkashin Ministoci.
Wata takarda da ta fado hannun PREMIUM TIMES, wadda Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ya sa wa hannu a ranar 19 Ga Mayu, ta nuna damuwar gwamnati, ganin yadda wasu ministoci ke gigiwar tsige shugabannin ma’aikatu, wadanda ba su ne suka nada su ba.
Shugaban Kasa ke nada su kamar yadda ya ke nada su monistocin. Don haka wannan danyen hukunci da ministoci ke yi, ya na maida wa gwamnati hannun agogo baya, inji Boss Mustapha.
PREMIUM TIMES ta gano an aika da wannan gargadi ga kowane Minista, Shugabannin Sojoji, Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, da sauran su.
An kuma tura wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, wanda bai dade da kama aiki ba, wato Ibrahim Gambari.
A baya an sha samun sabani da kuma yawan cire shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da dama.
Buhari ya sa hannu kan Dokar Cin-gashin-kan Majalisar Jihohi da bangaren shari’a
A ranar Juma’a ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan Dokar Musamman ta Cin-gashin-kan Majalisar Dokokin Jihohi da bangaren shari’un fadin kasar nan.
A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya bai wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya umarnin cire wa Majalisar Dokoki da Bangaren Shari’a kudaden su daga asusun duk wata jihar da ta ki bin wannan umarni.
Wannan doka dai ta na nufin kudaden da gwamnatin tarayya ke bai wa Majalisar Jihohi da bangaren shari’a na jihohi 36 da Abuja, ba su kara makalewa asusun jiha, ana jekala-jekalar sai yadda gwamna ya ga damar bada kudaden.
Kakakin Yada Labarai na Ministan Shari’a, Abubakar Malami, mai suna Umar Gwamdu ne ya fitar da wannan sanarwa, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES, a madadin ministan.
Wannan doka mai suna Doka Ta Musamman Ta 10, Ta 2020, ta bai wa gwamnoni umarnin shigar sa Majalisar Dokokin da bangaren shari’a cikin kasadin kudi, tun tashin farko.
Tuni har an bada umarnin kafa kakkarfan kwamitin da zai aikin shimfida ka’idoji, sharudda, hakki da kan-iyakokin da kowane bangare ke da ikon cin-gashin-kai, kamar yadda dokar Sashe na 121 (3) na Dokar Najeriya ta 1999 ya tanadar.
Wannan doka ta haramta wa gwamnonin jihohi rike wa Majalisar Dokokin Jiha da bangaren shari’ar jihar dukkan hakkokin su.
Kuma dokar ta umarci duk gwamnan da ya ki bin dokar, to a Akanta Janar na Tarayya ya cire kudaden majalisa da na kotuna da alkalan daga kason kudaden da gwamnatin tarayya ke tura wa jihar a duk wata.