Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya (NEF) ta yi kira ga al’ummar Fulani dake kudancin Najeriya su gaggauta barin yankin su dawo gida Arewa, idan ana koransu daga inda suka zaune yanzu a yankin Kudu.
Hakazalika Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta yi kira ga gwamnonin Arewa su shirya karban Fulanin dake shirin dawowa gida daga kudu, domin sama musu kyakkyawan mazauni.
Waɗannan bayanai na kunshe ne cikin jawabin da kakakin kungiyar dattawan, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya fitar kuma aka rarraba shi ga manema labarai a Kaduna.
Wani sashen jawabin yace: “Idan mutanen wani sashe a kasar nan sun lashi takobin koran Fulani daga yankunansu, kungiyar na bada shawara kawai su koma Arewa.”
“Gwamnonin Arewa su gaggauta shirin tarban Fulanin da aka kora daga kudu karfi da yaji.”
A bangare guda, Mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo Igboho, ana zarginsa da kai hari wata rugar Fulani dake garin Igua, karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun.
Shugaban kungiyar makiyaya Miyetti Allah (MACBAN), na jihar Ogun, Alhaji Abubakar Dende, ya bayyanawa manema labarai cewa yanzu haka yaran Sunday Igboho sun banka wuta gidan Sarkin Fulanin Igua, Alhaji Adamu Oloru. “Sun kona gidajen dake garin da na Sarkin Fulani, Alhaji Adamu Oloru, dake Igua da yammancin ranar (Litinin),”.