Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kira ga gwamnoni da su buɗe wuraren ibada, waɗanda yanzu haka suke a rufe saboda tsoron yaɗuwar korona, yana mai cewa masallatai da coc-coci “wurare ne masu muhimmanci”.
“Wasu gwamnonin sun ce shagunan shan barasa suna cikin abubuwa masu muhimmanci amma sun ce ban da wuraren ibada, wannan ba daidai ba ne,” in ji Trump.
Ya ƙara da cewa: “Yawan addu’o’i muke buƙata a Amurka ba ƙarancinsu ba.”
Kazalika ya ci alwashin cewa zai buɗe su da kansa ko ba da son gwamnonin ba.
Shugaban ba shi da ikon yin hakan a doka, sai dai zai iya janye tallafin gwamnatin tarayya zuwa jihohin.
[covid-data]