Sterling ya zama dan wasa na uku da ya ci kwallaye akalla 100 a karkashin Pep
Raheem Sterling ya shiga fitattun wadansu yan wasa, bayan da ya zama dan wasa na uku, bayan Lionel Messi da Sergio Aguero, da suka ci kwallaye akalla 100 a karkashin Pep Guardiola, fagenwasanni.com ta rahoto.
Kwallon sa ta farko Sterling a karkashin dan Sifen din ta zo ne lokacin da ya zira kwallon farko a wasan da suka doke West Ham da ci 3-1 a Etihad a watan Agustan 2016, kuma tun daga wannan lokacin ya ci gaba da zama daya daga cikin fitattun yan wasa a Turai, bayan da ya ci kwallaye 90 ga babbar kungiyar ta Firimiya tun farkon kakar wasa ta 2017-18.