Dakarun rundunar Hadarin Daji karkashin sojojin sama na Najeriya sun hallaka kusan ‘yan bindiga 200 a jihohin Katsina da Zamfara.
Sojojin sun hallaka su ne a wani hari da suka kai ta sama a sansanonin ɓarayin da ke Mai’Bai da ke ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina da kuma sansanin Kurmin Kura a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a ranakun Juma’a da Asabar.
A wata sanarwa da Shelkwatar Tsaro ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twiitter, ta bayyana cewa an ƙaddamar da harin ne bayan an ɗauki lokaci ana tattara bayanan sirri inda aka gano ɓarayin na amfani da wuraren biyu a matsayin maɓuyarsu
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ɓarayin na amfani da maɓuyar ta su wajen dillancin shanun da aka sace.
Ko a ranakun Talata da Juma’a sai da rundunar Hadarin Dajin suka yi nasarar kashe ‘yan fashi 135 a wani hari da suka kai a Sansanin Abu Radde na ɗaya da na biyu, da kuma Dunya da ke ƙananan hukumomin Jibya da Ɗan Musa dukansu a Jihar Katsina, a cewar shelkwatar tsaron.
Waɗannan hare-haren sun biyo bayan wani umarni da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar a makon da ya gabata na kakkaɓe ‘yan bindigar da suka addabi jihar Katsina.
Jihar wadda ita ce mahaifar shugaban kasa na cikin jihohin Najeriya da ɓarayi da kuma masu garkuwa da mutane suka addaba.
Ita ma jihar Zamfara a baya al’amura sun lafa dangane da batun ‘yan bindiga da kuma ɓarayi da suka addabi jihar, sai dai da alama hannun agogo ya fara komawa baya.