Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Kano Abdullahi Abbas Zai Gurfana A Gaban Sifetan Ƴan Sanda Na Ƙasa
Jam’iyyar PDP a jihar Kano, ta rubuta takarda zuwa ga babban sifetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Mohammed Adamu, tana buƙatar ya gurfanar da shugaban riƙon jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a gabansa bisa kalaman tunzura al’umma da yakeyi, wanda zasu iya kawo tashin hankali, kuma barazana ne ga tsaro.
‘’Kukai farmaki tare da hukunta duk wanda zaiyi satar kuri’a a zaben 2023. Ku ɗauki hukunci a hannunku babu abinda za’ayi. Na baku umarni ku hukunta duk wanda kuka gani yana ƙoƙarin maguɗi, hukunci na ne, kuma babu abinda zai faru.”
‘’Ina kira ga matasanmu na jam’iyyar APC, su adana makamansu a yanzu, kafin lokacin amfaninsu yazo.” Saƙon Abdullahi Abbas kenan ga mutanen APC, yayin bikin rantsuwa ga shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, wanda aka gudanar ranar juma’a, a filin wasa na Kano Pillars.
Shehu Wada Sagagi, shine shugaban jam’iyyar PDP a jihar Kano, yace sun miƙa takarda ga babban sifetan ƴan sanda na ƙasa, Mohammed Adamu, da sauran hukumomin gwamnati, duk da cewa ba suyi mamakin kalaman nasa ba, domin ɗabi’arsa ce furuci na tunzuri, a cewar Sagagi.
‘’A garemu dai babu inda kalamansa zasuyi mana illa, kuma ba zasu canja mutanen jihar Kano daga zaɓen abinda yake shine muradinsu ba. Bayan haka kuma ko domin ɗorewar dimokoradiyya, akwai buƙatar dole a magance yaɗuwar irin waɗannan kalaman tunzuri, wanda ko a baya bayan nan saida yayi irinsu akan jam’iyyar adawa.” Inji Sagagi
Da zamanin Nan zaiyi amfani ga talakka da ansama masa muhallali na zama kafin aure hakkin government ne tunda kuri’arsa ya bayar da bata lokacinsa akai Allah ya kwatarwa Dan Nigeria hakkinsa na gaskiya muggan shuwagabanni ya rabbill alamin