Yayin da jagoran mabiya Shi’a a Najeriya, Sheik Ibrahim El-Zakzaky ya cika shekara biyu tsare a Kaduna, hakan na nufin cewa:
Malamin ya yi azumi uku cur ya na tsare a Kaduna. Kuma an yi Sallolin Idi biyar ya na tsare a Kaduna.
Idan aka hada da zaman shekaru biyu da rabi da ya shafe a hannun jami’an tsaro a Abuja, El-Zakzaky ya yi Sallolin Idi 9 kenan a tsare.
Tsawon shekaru biyar cur da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan mulki, abu uku ne kawai suka wakana a kan idon malamin.
Na farko shi ne nada Shugabannin Tsaron Sojoji da Buhari ya yi, sai kuma kuma nada ministoci.
Abu na uku shi ne waki’ar da ta kusa shafe malamin a doron kasa, wadda har yau a kan ta ce ake ci gaba da tsare shi, duk kuwa da kotu ba sau daya ba ta taba bada belin sa.
Tun da aka tsare malamin har yau bai daina bayar da tallafin kayan abinci ga dimbin mabukata ba, a cikin kowane watan azumi. Premium Times ta tabbatar da haka.
Mai Rabon Ganin Badi: Da ya ke da sauran kwana a gaba, harbin da sojoji suka yi masa bai yi sanadiyyar ajalin sa ba. Haka kuma hargitsin da ya faru a Kurkukun Kaduna cikin Afrilu kafin azumi, bai ritsa da shi ba. Domin jami’an tsaro har mutum biyar a cikin daurarrun suka bindige.
Waiwaye:
A ranar 16 Ga Mayu, 2018, PREMIUM TIMES ta buga labarin kwatagwangwamar shari’a, zanga-zanga da tsare El-Zakzaky a Abuja da kuma dauke shi zuwa Kaduna.
Bayan gurfanar da Shugaban Mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, mabiyan sa sun rasa inda shugaban na su ya ke tsare.
Kokarin da lauyan babban malamin mai suna Maxwell Kiyom ya yi domin a bada belin wanda ya ke karewa ya ci tura, domin Mai Shari’a Gideom Kurada na Babbar Kotun Kaduna, ya ce ba za a tattauna batun beli baki da baki ba, sai dai ya rubuto a takarda.
Ba a dai fara sauraren kara ba a jiya Talata, saboda biyu daga cikin wadanda ake tuhumar ba a gabatar da su a kotun ta Kaduna ba.
A kotun dai dandazon jami’an tsaro sun hana magoya bayan El-Zakzaky da ‘yan jarida shiga ko matsawa kusa da harabar. In banda ma’aikatan kotun, ba a bar kowa ya shiga ba.
A wannan ne karon farko da aka fita da malamin tun bayan tsare shi da jami’an SSS suka yi cikin watan Disamba, 2015.
An gurfanar da shi da matar sa Zeenat ne a kotun Kaduna bisa zargi takwas da suka hada da kisa.
Yayin da a wurin hargitsin da ya yi sanadiyyar sojoji suka kashe mabiya malamin sama da 340, an samu rahoton kisan soja daya.
Yayin da har yau ba a tuhumi ko soja daya da laifin kisan mabiyan Sheikh El-Zakzaky ba, an gurfanar da malamin da matar sa bisa tuhumar su da laifin kisan soja daya da haddasa tashin hankali.
Daya daga cikin mabiyan malamin mai suna Abdulhamid Bello, ya bayyana cewa gwanmatin Najeriya ta guji aikata zalunci, domin shi zalunci kaikayi ne, a kan mashekiya ya ke komawa komai daren dadewa.
Ya ci gaba da cewa El-Zakzaky bai karbi sammacin karar da aka kai shi a Kaduna ba, ya ce sai an sake shi kamar yadda kotuna su ka bayar da umarni tukuna tun da farko.
A daya gefe kuma, mabiyan malamin na nuni da cewa ba su sani ba ko an maida shi Abuja a hannun SSS inda suke a tsare shi da matar sa, ko an tsare su a Kaduna.
Sai dai kuma sun jaddada cewa ko ma ina aka tsare shi, hakan ba zai hana su ci gaba da zanga-zanga a Abuja ba, har sai an sake shi kamar yadda kotu ta bayar da umarni.
KAKA-GIDAN MABIYA EL-ZAKZAKY KUSA DA FADAR SHUGABAN KASA
An shiga rana ta 889 kenan mabiyan sa na fitowa kan titinan Abuja sun a zanga-zangar neman a sakar musu jagora.
A kowace rana mazan su da matan su kan hau titina su na rera wakokin neman a sakar musu jagora da kuma la’antar gwamnatin da suke kira azzalumar gwamnatin da ta shanye musu jinin daruruwan ‘yan uwa.
Su kan yi macin da rawar kwamba tare kuma jerin gwanon yin sassarfa kan titi su na yi wa kwalta kirbin sakwara da kafafun su.
Daga nesa masu wucewa a kan motoci ko masu wucewa nesa da hanya, har ma da unguwannin da ke nesa su na rika jin karar dukann kwalta da suke yi da kafafun su, ‘rididif, rididif, ridif, ridif.
Su na wannan didima da kafafun su cike da izza da nuna rashin kasala, tare da cewa “mu ke wahalar da jikin mu, amma wasu ke jin zafin abin da mu ke yi, ba mu ba.”
Ba sau daya ba, ba sau biyu ba kuma sun sha yin artabu da ‘yan sanda, wanda hakan ya yi sanadiyar kashe wasu masu zanga-zanga, ciki har da jagoran mabiyar, wato wakilin Sheikh El-Zakzaky na Sakoto, wanda aka sani da Malam Kasimu da kuma wasu daban.
A jajibirin da SSS suka fice da El-Zakzaky zuwa Kaduna, an yi artabu sosai tsakanin ‘yan sanda da mabiyan malamin a Dandalin Eagle Square da Sakateriyar Gwamnatin Tarayya, a Abuja.
Bayan kura ta lafa ne masu zanga-zanga suka rika shelar cewa sun ci gabala akan jami’an tsaron, domin sun gigice su na harbi, har suka yi kuskure suka harbi wani jami’in su da kan su, sun yi tsammanin mai zanga zanga ne.
An kuma nuno hoton wata wata motar jami’an tsaro da masu zanga-zanga suka yi wa kwatsa-kwatsa, har suka rubuta, “FREEE EL-ZAKZAKY” da jan fenti a kan motar.
SHI’A FREE EL-ZAKZAKY
Tun da jijifin safiyar Talata suka rika yada sanarwar cewa sun samu labarin an dauke jagoran na su daga Abuja, da misalin karfe 4 na asubahi, aka nufi da shi Kaduna tare da matar sa, domin a gurfanar da su kotu.
A Kaduna ma a lokacin da ake zaman kotu, har bayan kammala shari’a, mabiyan sun yi zanga-zangar neman a sake shi.
Kamar yadda a Abuja jiya Talata dimbin mabiyan maza da mata sun sake hawan kwalta a Sakateriyar Gwamnatin Tarayya, suka ci gaba da zanga-zangar sai-Baba-ta-gani.
SHAWARWARIN A SAKI EL-ZAKZAKY
Cikin watan Afrilu, jaridar Daily Trust ta yi sharhin da ta bayyana ra’ayin ta cewa ta na bai wa gwamnatin Buhari shawara da a saki El-Zakzaky, domin kauce wa sake mummunan rikici mai kama da na Boko Haram a Najeriya.
Shi ma tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya yi kakkausan gargadi ga gwamnatin Najeriya da ta gagguta sakin malamin domin gudun abin da ka iya biyo baya idan tura ta kai magoya bayan sa bango.
An gurfanar da El-Zakzaky kotu, kwana daya bayan da sojojin Isra’ila suka kashe Falasdinawa sama da 50.
Ganin yadda ‘yan Najeriya ke ta nuna jimamin kisan Falasdinawan, daya daga cikin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky a Abuja mai suna Yusuf, ya ce “idan an tuna ai Malam zakzaky ne kan gaban mazahara idan ana maganar makomar Falasdinawa.
“Amma an wayi gari a Najeriya ba a ganin laifin gwamnatin Buhari da ta kashe daruruwan musulmi mabiya mutumin da ya fi kowa nuna damuwa idan an kashe Falasdinawa.
“Don munaficci dan Najeriya zai rika kumfar baki an kashe musulmin wata kasa, wadanda da yawn su ma mabiya Shi’a ne a can. A nan kuma an kashe mu amma su na murna, don mu ‘yan Shi’a ne.’’
TSAKA MAI WUYA
Gwamnatin Muhammadu Buhari na cikin tsaka-mai-wuyar fama da rigingimu tun bayan hawan sa mulki.
Watanni shida bayan hawan sa, rikici ya barke a Zaria tsakanin mabiya Sheikh El-Zakzaky da sojoji tagwatar Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya a lokacin, Janar Tukur Buratai, inda aka yi mummunan kisa, har suka shiga cikin gidan malamin.
Bayan an kashe mutane a cikin gidan sa, an kuma kashe ‘ya’yan sa hudu. An nakasa masa ido daya kuma na ji masa raunuka.
Matar sa Zeenat kuwa lauyan su ya tabbatar da cewa har yau akwai harsasai a cikin jikin ta.
Kafin zaben 2015 kuwa, a fili ta ke cewa duk da malamin babu ruwan sa da shiga harkar zabe ko siyasa, ya nuna fifikon Buhari a kan Jonathan.
Cikin wata hira da jaridar RARIYA ta yi da El-Zakzaky a farkon 2014, malamin ya yi amanna cewa a dukkan takarar da Buhari ya yi sau uku a baya, da bai yi nasara ba, duk magudi aka yi masa.
Gwamnatin Buhari na fama da matsalar kashe-kashe bakatatan a Arewacinn kasar nan, musamman a jihohin Zamfara, Kaduna, Benue, Nasarawa da Taraba.
Har yanzu Boko Haram sun zame wa gwamnatin Buhari tamkar hakin tofa, domin a kullum kashe su ake yi, kuma ana cewa an gama da su, amma kuma kullum ba su daina kai hare-hare ba.
Duk da cewa mulkin farar hula ake yi, amma sama da rabin jihohin kasar nan duk sojoji ne kan gaba wajen sa-idon kula da tsaro, saboda tashe-tashen hankulan da ake fama da su.
Irin yadda ake girke sojoji a cikin yankunan jihohin kasar nan, bai hana ci gaba da yin garkuwa da mutane ba a yankuna daban-daban.
Sau da dama ‘yan fashi sun daina tare hanya, sun fi karkata ga shiga kananan garuruwa da kauyuka kan su tsaye, saboda matsalar tsaro.
A kullum sai kara girka sansanonin sojoji ake yi a yankunan da tashe-tashen hankula suke ci gaba da kamari.
Duk da kirke sojojin da ke ci gaba da yi, hakan bai kawo alamar karshen kashe-kashen da ake fama da su ba, musamman a Arewacin kasar nan.
Irin yadda ake yawan kama muggan magamai daga hannun mahara a kullum a Arewacin kasar nan, ya nuna cewa akwai matsala kwance a kasa sosai.
A Babban Birnin Tarayya, Abuja kuwa, mabiya Sheikh El-Zakzaky a kullum sai kara tudadowa suke yi, su na yin zaman dirshan na zanga-zangar neman a sakar musu jagora.
Tun a na bin su a guje su na tserewa, yanzu sun kai ga dakewa, ana artabu da su da jami’an tsaro, duk kuwa da ba su dauke da ko da bindiga balle sanda ko gora. Sai dai duwatsu kawai.
A yau sun cika kwanaki 890 cif su na zanga-zanga a Abuja.
Tsakanin inda ake artabu da su da Fadar Shugaban Kasa, bai kai tazarar kilomita daya tal ba.
A zaman yanzu dai Mai Shari’a Kurada na Babbar Kotun Kaduna ya daga kara zuwa 21 Ga Yuni, 2018.
Mayu, 2020: Shari’a Ba Ta Kare Ba, Babu Beli, Magoya Baya Ba Su Fasa Zanga-zanga A Abuja Da Kaduna Ba
Babu irin matakan da jami’an tsaro ba su dauka ba, domin hana mabiyan Sheikh El-Zakzaky ci gaba da zanga-zanga a Abuja.
An kama na kamawa, an raunata, an fesa ruwan zafi, an bude wuta, an harba barkonon-tsohuwa, amma har zuwa daf da karshen azumin nan na shekarar 2020, ba su daina zanga-zanga a cikin izza a Abuja, babban birnin tarayya ba.
Kamar yadda gwamnati ta nuna babu rana ko lokacin sakin jagoran na su daga kurkukun Kaduna, haka mabiyan na sa su kuma ke ci gaba da nuna cewa zanga-zanga babu ranar dainawa, har zai El-Zakzaky ya kubuta.