An bayyana cewar halin da sha’anin tsaro ya shiga a kasar nan yanzu, lamari ne da ya kamata jama’ar kowa da kowa a haɗa kai domin samun mafita, amma ba kawai a ɗora laifi kacokan akan Shugaban kasa ba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani a jigo a jam’iyyar APC mai mulki Alhaji Usman Ibrahim Sardaunan Badarawa, a yayin tattaunawar da ya yi da wakilinmu a garin Kaduna.
Sardaunan Badarawa ya ƙara da cewar a fili yake Shigaban ƙasa Buhari na iyaka bakin kokarin shi wajen saita kasar bisa turba, amma sai dai abin nan da Hausawa ke fadi na cewar Hannu daya ba ya ɗaukar jinka,a bisa ga haka sauran Shugabanni su ma kamar Gwamnoni da Shugabannin kananan hukumomi ya kamata su mike a haɗa hannu domin tunkarar matsalar gaba ɗaya.
Ɗan siyasar ya ƙara da cewar ta la’akari da yadda harkar tsaro ke da muhimmanci ya sanya shi ɗaukar nauyin sanya fitilu masu amfani da hasken rana a yankin mazaɓar shi ta Kaduna ta Arewa, domin taimakawa jami’an tsaro saukin gudanar da ayyukan su cikin sauki.
Usman Ibrahim wanda ya taɓa zama Shugaban ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, kuma ya yi takarar Kujerar Majalisar Dattawa mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya a zaɓen da ya gabata, ya yaba hoɓbasa na mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i bisa ga ayyukan alheri da yake ta faman yi a jihar, inda yace wannan abin alfahari ne a garesu matsayin su na ‘yan jam’iyyar APC, kuma zai zama sharadi ga duk wanda zai nemi gwamna a jihar dole ya biyo sahu na gwamna El Rufa’i.
Usman Ibrahim ya kuma nuna jin daɗin shi da yadda aikin sabunta rijistar ‘ya’yan jam’iyya ke gudana, inda yace ko shakka ba ya yi akan irin
Farin jinin da jam’iyyar APC ke dashi, wanda hakan ya sanya dubun dubatar mutane suka fito domin sabunta rijistar.