Rundunar sojin Najeriya ta sanar da Burgediya Janar Mohammed M. Yerima a matsayin sabon kakakinta, kamar yadda wasu kafofin yaɗa labaran kasar suka ruwaito.
Yerima zai maye gurbin Burgediya Janar Sagir Musa wanda ya riƙe muƙamin a shekaru biyun da suka gabata.
Kafar yaɗa labarai ta PR Nigeria ta ruwaito cewa wannan ne na farko cikin sabbin naɗe-naɗe da sabon hafson sojin ƙasar Majo Janar Ibrahim Attahiru zai yi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Brig Janar Yerima mutumin ƙaramar hukumar Bade ne a jihar Yobe.
Ya yi karatun kimiyyar Siyasa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria sannan a shekarar 1989 ya shiga aikin soja.