Mahukuntan sojojin Najeriya na binciken tuhumar wani soja mai suna Mohammed Abddullahi, wanda ya soki karin wa’adin shugabancin da aka yi wa Shugabannin Hafsoshin Najeriya.
Abdullahi, wanda ke da mukamin ‘Staff Sergeant, ya caccake shugabannin sojojin tsaron kasar nan a soshiyal midiya, abin da bai yi musu dadi ba.
Ya soki lamirin yadda aka kara musu wa’adi, duk kuwa sun dade a kan mukaman, abin da ya hakan zai iya kashe kwarin guiwar kananan sojoji a kasar nan.
Sergeant Abdullahi mai lambar dauka aikin soja kamar haka: 97NA/44/315, ya soki dadewar da Manyan Hafsoshin suka yi ba tare da an cire su an nasa wasu ba.
Kwakkwarar majiya ta ce Sashen Leken Asiri na Sojoji ya na bincikar sojan, kuma sakamakon da ya fitar ne za a yi amfani da shi a tuhume shi.
Wannan majiya dai ta ce tun cikin watan Fabrairu ne Buratai ya bada umarnin a binciki sojan wanda ya ragargaje su a soshiyal midiya.
Dokar Tsarin Aikin Soja ta 2018 dai ta haramta wa soja ya shiga soshiyal midiya ya yi wasu maganganun da suka kauce wa tsarin aikin soja.
Shugaba Muhamadu Buhari ya nada Manyan Hafsoshin Najeriya su hudu, wato na tsaro, na soja, na sojan ruwa da na sojan sama ranar 13 Ga Yuli, 2015.
A ka’ida Buhari zai nada su ne tsawon wa’adin shekaru biyu. Amma zai iya kara musu shekaru biyu bayan biyun farko.
Buhari ya kara musu wa’adin shekaru biyu kowanen su cikin 2017. Amma kuma a lokacin yawancin su lokacin yin ritayar su ta yi.
Cikin 2019 kuma Buhari ya kara musu wa’adi, abin da ya jawo surutai a kasar nan, har Abdullahi soja ya soki lamarin.