Nazari Tareda Hasashen Wasa Tsakanin Ayau Lahadi Real Madrid Da Valencia.
ayau za’a fafata wasan mako na 23 a gasar La Liga, inda babban wasa a makon shine karawa tsakanin Real Madrid da Valencia.
Real Madrid Zata karbi bakoncin Valencia a yau Lahadi da karfe 4:15 a filin wasa na Alfredo De Stefano.
Real Madrid tana mataki na 3 a teburin gasar La Liga dauke da maki 46 bayan wasanni 22 data fafata, inda tayi nasara a wasanni 14 canjaras 4 rashin nasara 4.
Valencia tana mataki na 12 a teburin gasar La Liga dauke da maki 24 bayan data fafata wasanni 22 tayi nasara 5 canjaras 9 rashin nasara 8.
Abun dubawa nafarko shine Valencia bata taka rawar gani a kakar wasa ta Bana duba da iya wasanni 5 kacal da lashe cikin wasanni 22 data fafata, inda Real Madrid ta lashe wasanni 14 cikin 22 data fafata.
Sai a haduwar kungiyoyin biyu da junan su zamuga a wasanni 5 da suka gaba Real Madrid ta doke Valencia sau 2 anyi canjaras 1 Valencia ta samu nasara sau 2.
Wasanni 5 na karshe da Real Madrid ta fafata a gasar La Liga tayi nasara a wasanni 3 tayi canjaras 1 rashin nasara 1.
Haka itama Valencia wasanni 5 na karshe data fafata tayi nasara a wasanni 2 canjaras 2 rashin nasara 1.
Wasannin da Real Madrid Zata fafata na gaba a gasar La Liga inaganin ba wasannine masu zafi ba, inda zata fafata da Real Valladolid da Kuma Real Sociedad, sai dai akwai Dan Kalubale a wasan ta Real Sociedad.
Ita Kuma Valencia wasanni ta biyu na gaba zata fafata ne da Celta Vigo da Kuma Villarreal, idan aka kwatanta Dana Real Madrid ina Ganin kamar na Valencia sun fi zafi.
To gaskiya kowacce kungiya tana bukatar maki musamman ma Valencia saboda inhar kungiyar ta sake tayi rashin nasara tofa zata koma mataki na 15 a gasar La Liga inhar Getafe da Cadiz da Osasuna sunyi nasara a wasannin su, sakamakon dukkannin su Makin su 24 ne Osasuna Kuma 22.
Idan Kuma Valencia tayi nasara to fa zata koma mataki na 11 ne inhar Athletic Bilbao tayi rashin nasara a hannun Osasuna.
Ita kuwa Real Madrid tana daidai da takwarar ta wato Barcelona ne a mataki na 2 da na 3 dauke da maki 46.
Kungiyar ta Real Madrid inhar ta samu nasara a yau zata koma mataki na 2 a teburin La Liga dauke da 49.
A cikin su kowa na bukatar maki, sai Haduwar su takarshe Valencia ta doke Real Madrid da ci 4-1, ina Ganin Real Madrid Zata so ta dakile yunkurin Kara yin rashin nasara Karo biyu a jere a hannun Valencia.
Menene Harsashenka