Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta fitar da sunayen ma’aikata bakwai da suka mutu a hatsarin jirgin, Beechcraft KingAir BB305i a jiya.
Jami’an da suka mutu sun hada da: Laftanar Jirgin Sama Haruna Gadzama (Kyaftin); Laftanar Sama Henry Piyo (Co-Pilot); Jami’in tashin jirgi Micheal Okpara da Jami’in Garanti Bassey Etim.
Sauran sun hada da: Sajan Olasunkanmi Olawunmi da Sajan Ugochukwu Oluka da kuma Warrant Officer Adewale Johnson (Onboard Technician).
Wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a da Watsa Labarai na Sojan Sama na Najeriya ya fitar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, ya ce: “Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta tabbatar da cewa jiragin nata, kirar Beechcraft KingAir B350i (NAF) 201), ya fadi ne yayin da yake dawowa zuwa Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na kasa da kasa na Abuja bayan da ya samu matsalar rashin inji.
Yace “Kamar yadda bayani ya gabata, babban hafsan sojan sama (CAS), Air Vice Marshal Oladayo Amao, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Ya kara da cewa: “ CAS ta ziyarci inda hatsarin ya faru, tare da mai girma Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya); Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika; Babban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor, da sauran shugabannin hafsoshin soja.