A yayin da ake ta ce-ce-ku-ce game da masu fitowa su zagi Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW, wasu malaman addinin musulunci sun fito sun bayyana matsayar addini.
Daga cikin wadanda su ka yi magana a game da wannan batu akwai tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II wanda aka tunbuke daga gadon sarauta a watan Maris.
Muhammadu Sanusi II ya na yin karatun addini a gidansa da ke Legas a cikin wannan watan Ramadan mai alfarma. A wajen karatun ne aka bijiro masa da wannan magana.
Wasu Bayin Allah sun aikowa Sanusi II tambaya game da hukuncin wanda ya zagi Annabi Muhammad tsira ga amincin Allah ya tabbata gare sa, inda shi kuma ya bada amsa.
Tsohon sarkin ya ke cewa zagin Manzon Allah SAW zai jawowa mutum kisan kai. Mai martaban ya ce a iyaka fahimtarsa malamai sun yi tarayya a kan kashe wanda ya zagi Manzo.
Sanusi II ya kafa hujja ne da fatawar babban malamin musulunci Ahmed Ibn Al-Halim Ibn Taymiyyah wanda ya ce duk malamai sun hadu a kan kashe wanda ya zagi Annabi.
A wani littafi da Ibn Taymiyyah ya rubuta mai suna zararren takobi a kan wanda ya zagi Manzon Allah, domin kare Annabi Muhammad, ya ce kisa ta hau kan wanda ya taba Annabi.
Mai martaba Sanusi II ya amsa wannan tambaya ne a ranar 1 ga watan Mayu a yayin karatun da ya ke ya na littafin Madarij Salikeen na shehin Malami Ibn Qayyim Al-Jawziyyah. Ko da mai martaba bai yi karin bayani game da wannan mas’ala ba, sai dai bincike a littafin ya nuna cewa bajiman malamai sun bada hukuncin kashe wanda ya zagi Annabi SAW.
Daga cikin magabatan da su ke da wannan ra’ayi akwai Malik, Layth, Ahmad Hambal, Ishaq Ibn Rahaway, Ash Shafi. Su ka ce haka hukuncin ya ke a kan musulmi da kuma kafiri.
Amma Abu Hanifa ya na kan ra’ayin cewa idan kafiri ya na biyan jizya, ba za a kashe shi ba. Sauran malaman sun tafi a kan cewa ko da mutum ya tuba, za a zartar masa da kisa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: info@dailyepiers.com.ng