- TA’ADDANCI: Muna Fasa Shugunan Mutane Mu Kwashi Wayoyi Ne Domin Mu Sayi Shaddodi Na Kece Raini A Wurin Biki
Biyo bayan samun bayanan sirrin da kungiyar ‘yan sintiri dake Unguwar Sharada suka samu akan masu fasa shaguna suna satar wayoyi, tuni dai rundunar ‘yan Vigilante din suka gudanar da wani babban sintiri, inda suka sami nasarar kama wasu matasa biyu bisa zarginsu da satar Injina da wayoyi.
Inda aka kama su da injina guda 4 da wayoyin hannu wanda suka tabbatar da cewa suna fasa shagunan masu cajin waya da zarar dare ya yi, inda suke daukar wukake su shiga gudanar da aikinsu.
Matasan sun bayyanawa wakilin mu cewa azal ce kawai ta hau kansu domin kuwa wannan shine na farko.
Jim kadan bayan kama su hakan tasa suka bayyana hujjarsu karara, inda suka ce sun yi haka ne sakamakon wani biki da za su yi kuma ba su da kudin da za su sayi shadda ta kece raini sabo da gudun kar a ji kunya.
Kwamandan ƙungiyar ƴan Sintiri Alh. Amada Sharada ya bayyana cewar sun dade suna fuskantar wadannan matsalolin a yankin nasu, wanda hakan ta sa ya shirya wani fatiro kuma suka sami nasarar kama wadannan matasa, inda ya ja hankalin iyaye da su kara sanya Idanu akan ƴaƴansu domin zamani ya sauya.