Morocco ta Sake Lashe Gasar Afrika ta ‘Yanwasan Gida
Ƙungiyar ƙwallon ƙafan maza ta ‘yan wasan gida ta ƙasar Morocco ta sake lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika ta ‘yan wasan gida wato CHAN a daren jiya Lahadi.
Ta sake lashe gasar ne bayan da ta doke ƙungiyar ƙwallon ƙafan maza ta ‘yan wasan gida ta ƙasar Morocco daci 2 da nema a birnin Younde na ƙasar Cameroon wadda ita ce ta karɓi jagorancin gudanar da gasar ta bana.
Wannan shine karon farko da aka sami ƙasar da ta lashe wannan gasa sau biyu a jere kenan tun bayan lokacin da aka fara gudanar da ita a shekarar 2009 wato shekaru 12 kenan da suka gabata.
A waccan gasar da aka kammala ta baya Morocco ce ta zamo zakara wadda daman ita ce ta ɗauki nauyin gasar kuma ta lashe abarta, yanzu ma gashi ta sake lashewa bayan da ta wanke ƙasar Mali daci 2 da nema.