Daga Alhussain Suleiman
Amsawar Dakta Jamil Zarewa, Jami’ar ABU Assalamu alaikum. Malam barka da warhaka, da fatan kana nan lafia. Malam mene ne hukuncin wanda ya yi azumi amma bai yi buxabaki ba, ma’ana bai sha ruwa bayan ladan ya kira sallah ba, sai kawai ya yi jima’i da matarsa, ma’ana maimakon ya ci wani abu ko ya sha, sai ya fara da yin jima’a, shin yaya azuminsa?.
Wa alaikum assalam, Azuminsa ya yi daidai, mutukar ya sadu da ita ne bayan rana ta fadi. Annabi s.a.w ya yi umarni a yi buda baki da dabino ga wanda ya samu dama, in ba hali kuma a yi da ruwa kamar yadda ya tabbata a Hadisai.
Abin da ya gabata yana nuna cewa: Yin buxa-baki da dabino ko ruwa shi ne sunna, saidai wanda ya fara da jima’i azuminsa ya inganta, tun da Allah ya halatta masa jima’i a daidai wannan lokacin kamar yadda aya ta: 187 a suratul Bakara ta nuna hakan.
Allah ne mafi sani. Ina Fama Da Ciwon Qoda, Zan Iya Ciyarwa A Maimakon Azumi? Assalamu Alaikum malamina inada tambaya, mace ce bata da lafiya, ciwon koda ya fara tsananta gare ta, sai satinnan likitoci suka bata shawara duk bayan minti talatin ta ci wani abu daga Abinci amma kar ta qoshi, to malam yaya za’a billowa maganar Azumin da ta sha, ciyarwa za’a cigaba da yi ko jira za’a yi sai ta warke ta rama? Wa alaikum assalam, in har tana tunanin samun sauqi kafin wani azumin ya zo, ba za ta ciyar ba, za ta bari ta rama bayan ta samu dama, saboda aya ta: 184 a suratul Baqara ta nuna cewa: wajibin mara lafiya shi ne rama azumin da bai yi ba na Ramadhana bayan ya samu dama a wasu kwanakin.
Matukar likitoci sun tabbatar ba za ta samu sauqin da za ta rama azumi daga baya ba, ya halatta ta ciyar a maimakon kowacce rana. Allah ne mafi sani.
Mace Za Ta Iya Yin I’itikafi ? Assalamu Alaikum, malam menene hukuncin i t t i k a f i n m a t a a musulunchi? Wa alaikum asssalam, ya halatta mace ta yi i’itikafi,
saboda matayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun yi i’itikafi kamar yadda ya zo a sahihil Bukhari.
Yana daga cikin ka’idoji a usulul fiqhi duk hukuncin da ya zo a sharia yana hade mata da maza, sai idan an samu dalilin da ya kebance maza kawai.
I’itikafi ibada ce tabbatacciya a musulunci wacce Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aikata ta saboda neman kusanci da Allah a watan Ramdhana, babu bambanci tsakanin mace da namiji wajan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wannan ibadar, saidai kar matar aure ta fita sai ta nemi iznin mijinta.
Allah ne mafi sani. Yaushe Ake Fita Daga I’itikafi? Assalamu Alaikum. Malam ina so a fada min mafi rinjayan zance game da lokacin fita daga I’itikafi? Wa’alaikumus salam, to xan’uwa malamai suna da ra’ayoyi biyu akan wannan mas’alar :
- Fita daga I’iitikafi daga zarar an ga watan Ramadhna, wato bayan rana ta faxi a daren Idi, saboda i’itikafi ana yinsa ne a Ramadhana kuma idan an ga wata, Ramadhana ya kare.
- Mai I’itikafi zai iya zama har zuwa lokacin sallar Idi, ta yadda zai fita bayan kammala sallar, Imamu Asshafi’i yana cewa: “Duk wanda ya yi niyyar koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi to ya fita daga i’itikafi bayan rana ta fadi in an ga wata, watan ya yi nusan ko ya cika, amma in ya zauna zuwa sallar idi, hakan shi ne yafi” Imamu Malik yana cewa:
“Na samu labarin wasu daga cikin mutanan kirki suna fita daga I’itikafi bayan sallar idi”. Zance mafi inganci shi ne fita daga i’itikafi bayan ranar daren idi ta fadi, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana i’itikafin dararen goman qarshe ne, su kuma suna fita idan daren IDI ya shiga.
Don neman qarin bayani duba Al-majmu’u na Nawawy 6/323 da kuma Fataawa Allajnah Adda’imah 15/411. Allah ne mafi sani.
Allah Bai Qayyade Lokacin Rama Azumi Ba! Assalamu alaikum, Dr. Mace ce ta sha Azumin shekara uku ajere saboda ciwon ulcer, kuma abin da zasu kai baki gagararsu
yake ballatana ta ciyar, Menene mafita? Wa alaikum assalam ta jira har Allah ya bata lafiya sai ta rama, Allah maxaukakin sarki a cikin Suratul Baqara aya ta: (185) ya sanya ramuwar azumi ga mara lafiya a wasu kwanaki na daban don ya nuna abin a bude yake, zuwa lokacin da aka samu dama, ba tare da yin sakaci ba.
Allah ne mafi sani. Muna Jinkirta Wankan Janaba Zuwa Bayan Asuba, A Watan Ramadana, Yaya Hukuncin? Assalamu alaikum, malam ina da tambaya shin meye hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin azumi, amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito, shin yaya matsayin azumin su yake? Na gode.
Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da mijinta su jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan Ramadhana, Azuminsu kuma ya inganta, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yakan yi haka da matansa, kamar yadda iyalansa A’isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma Muslim ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 1874. Allah ne mafi sani.
Za A Iya Fitar Wa Da Kirista Zakkar Fidda Kai? Assalamu alaikum, Ina yiwa malam fatan alkhairi, Allah ya qara budi, wasu ne suke neman fatawa akan wannan mas’alar “musulmine yake auren Christian, to wai idan zai fidda zakkar fidda kai itama zai fitar mata?” Wa alaikum assalam, Hadisi ya tabbata daga Ibnu Umar cewa: “Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farlanta zakkar fid-dakai akan kowanne
musulmi Da ne ko bawa” kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito. Hadisin da ya gabata yana nuna musulmi ake fitarwa zakkar fid-dakai, amma kafiri ba’a fitar masa, kuma ba’a shi in an fitar. Allah ne mafi sani.
Zan Iya Bada Kuxi Maimaikon Abinci A Zakkar Fidda-Kai? Assalamu alaikum Dr. shin ana iya bada kuxi a zakkatul fitr maimakon kayan abinci? Wa alaikum assalam, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya wajabta zakkar fidda sa’i na dabino ko Sha’ir kamar yadda ya zo a hadisin Ibnu Umar wanda Muslim ya rawaito a lamba ta: (2287).
Abin da Malamai suka fahimta a hadisin da ya gabata shi ne ana fitar da zakkar fiddakai ne daga abin da mutanen garinku suka fi ci kamar Shinkafa Dawa Masara a wajan ‘yan Nigeria, Fukaha’u sun yi savani game bada kuxi a maimakon abincin da ya zo a hadisi :
- Umar Dan Abdulaziz da Abu-hanifa da Ibnu-taimiyya da Albani da wasu magabata sun tafi akan halaccin bada kuxi a maimakon zakkar fiddakai saboda abin da yasa aka shar’anta zakkar fid-dakai shi ne: wadatar da talakawa daga barin roqo a ranar IDI hakan kuma yana tabbata ta hanyar bada kuxi ko qimar abincin.
- Ya wajaba a fitar da abincin da mafi rinjaye suke ci, saboda tun da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fadi sunayen abinci, hakan sai ya nuna su yake so a fitar ba qimarsu ba, kamar yadda yake a hadisin Ibnu Umar wanda ya gabata. Zance na biyu ya fi inganci saboda bin sunnar Manzo shi ne daidai, tare da cewa in an samu lalura
ta qarancin abinci ko kuma talakawa suka nuna sun fi buqatar kuxi ya halatta a fitar da kuxin ko qimar abincin a maimakonsa, saboda akwai hadisai da suke nuna halaccin amsar qima a babin zakkar dabbobi in SA’I bai samu dabbar da ya kamata ya amsa ba.
Don neman qarin bayani duba: Al-mabsud 2/156 da kuma Al’istizkaar 9/346 da kuma Al’iktiyarat Alfiqhiyya lil’Albani na Abu-shaxy shafi na 209-210. Allah ne mafi sani. Hukuncin Haxa Sittu Shawwal Da Ramuwar Ramadan Malam idan ana binka ramuwar azimi za ka iya niyya biyu, wato da nufin sittu shawwal da kuma ramuwar Ramadhana a lokaci guda ? Don Allah malam taimaka min da bayani.
To ‘yar’uwa kowanne daban ake yinsa, saboda manufarsu ta bambanta, don haka ba za’a haxa su da niyya xaya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma’a, za mu fahimci hakan a cikin faxin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : “Duk wanda ya azumci Ramadhana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara” Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu- shawwal daban. Faxin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:“Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal” ya sa wasu malaman sun tafi akan cewa : bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan, kamar yadda ya zo a : sharhurmumti’i 6\443. Allah ne mafi sani.