Lissafin da masana ilimin taurari suka yi a Saudiyya ya nuna cewa abu ne mai wuya a ga jaririn watan Shawwal na Karamar Sallah a yammacin ranar Juma’a, ranar da azumi yake cika 29.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito hasashen da suka yi na nuna cewa wata zai riga rana faɗuwa ranar Juma’a, saboda haka ranar Idi ita ce Lahadi 24 ga watan Mayu, yayin da za a yi azumi 30.
Wata cibiyar masana taurari ce a Saudiyya da ke Jami’ar Majmaah a kusa da birnin Riyadh ta bayyana hakan.
Cibiyar binciken ta ce: “Bisa hasashen da masana ilimin taurari suka yi wanda aka wallafa, ya ce rana za ta faɗi da ƙarfe 6:39, yayin da wata zai faɗi da ƙarfe 6:26 ranar Juma’a. Hakan na nufin wata zai faɗi minti 13 kafin rana ta faɗi.
“A ranar Asabar, 30 ga watan Ramadana, daidai da 23 ga Mayu, rana za ta faɗi da ƙarfe 6:40 sannan jaririn wata ya faɗi da ƙarfe 7:23, abin da ke nufin watan zai ci gaba da kasancewa har tsawon minti 43 bayan faɗuwar rana,” a cewar cibiyar.
A gefe guda kuma, Dr. Abdullah Al-Mosnad, Farfesa a sashen Kimiyyar Ƙasa na Jami’ar Al-Qassim, ya jaddada cewa wata zai faɗi minti 10 kafin rana a ranar Juma’a a birnin Makkah, saboda haka sai ranar Lahadi za a yi Idi bayan cikar azumi 30.