Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma manajan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Gbenga Daniel, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ana sa ran Daniel zai karbi katin zama dan jam’iyyar APC kafin a rufe rajistar sabbin mambobi a yau.
Wata majiya tace tsohon gwamnan na jihar Ogun zai gana da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a ranar Laraba.
Wanda ake sa ran zasu kasance cikin taron sun hada da gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, da Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da Badaru Abubakar na jihar Jigawa.