Daga A’isha Muhammad Kazimiyyah
Mu’amalar aure kala kala ce, amma mu’amalar auren Malam Bahaushe a gidan aure ta daban ta ke. Babban jarabawa be ga mace a wannan zamanin irin zamantakewar aure musamman ta Malam Bahaushe.
Malam Bahaushe a kwai abin daya xauki mace dashi a cikin gidan sa, shi ne mace ita wata aba ce da idan yana da wata buqatu zai biya kawai a gurinta, da zarar ya gama kammala biyan buqatunsa a wajen ta kuma shikenan .
Sai dai acikin al’adar Malam Bahaushe a gidan aure kala-kala ne, shi wani kawai abin daya dauka shi ne aure tamkar saka riga ne, ka saka ka cire faqat. Duk wanda ya gadama zai saka, kuma duk wanda ya ga dama zai cire.
Bai dauki aure a bakin komai ba. A gidan Auren Malam Bahaushe, mace bat a da wani ‘yanci na karan kanta wanda za ta yi taqama dashi.
Illah iyaka ta kasance cikin yin bauta da reno da tuwo da sauran ayyukan cikin tsakar gida.
Mace bata da wani iko a cikin gidan Malam Bahaushe sai abin da maigidanta ya ce, ba a shawara da ita, ba’a neman wani taimakonta idan ba na fannin aikatau ba.
Babu rayuwa ingantacciya a tare da zaman auren su , bas a zaman tadi bare gar a nemi agajin tat a wajen shawara. Wani ma gani yake idan ya yi taxi da matarsa kamar zata raina sa.
Alhalin kuma bahaka ba ne. Mace a rayuwar auren Malam Bahaushe ita ‘yar kallo ce, duk wani hakkin nata da ‘yancinta da Allah ya bata an tauye mata shi.
A sanin kowa ne cewa; Allah ya yi hani ga zalunci kuma ya na son masu tausayi da adalci a rayuwarsu. Addin musulumci ya fitowa duk ko wace mace da haqqinta da gatanta.
Kafin zuwan musulumci mata sun fuskanci wulaqanci da kyama a rayuwarsu, kamar yadda ruwaya take nuna mana yadda wasu suka rinqa tauye hakkin mata ,ta wajen binne su da rai, ko rarsu daga gida, rashin bas u ‘yancin su.
Amma ya a kayi bayan zuwan Addinin Musulumci? Addinin Musulumci ya zo da yancin mata da kuma gargadi wajen cutar das u da ake .
kafin zuwan musulumci an musgunawa mata an tauye musu hakkin su, an maid a su wani abu tamkar mutum da dabba, ma’ana su mata ba a dauke su a matsayin mutane ba.
Hakan ya sa mata suka fuskanci nau’ika na zalumci da tauye hakkinsu. Misalin; killace su a gida tamkar fursunoni mai da su ababe mallaka wanda ta kai da har ana gadonsu. Musulumci da ya zo sai ya baiwa mata matsayi dai-dai da na mijin. Wato ya dai-dai ta su tare da na mjin ta wajen adamtaka ba tare da fifiko ba.
Sannan ya kwato musu hakki da aka tauye musu. Kuma ya toshe wata Baraka da ake ganin mace ba abakin komai ba. Ya toshe hanyar da wasu za su ci moriyar mace ba gaira babu dalili.
Kuma Musulumci ya baiwa mata hakkin nawajen sanya hijabi da neman ilimi da kuma hakkin sarrafa abin da suka karanta na daga wajen neman ilimin.
A ta dalin miye ne Malam Bahaushe zai kuntatawa Mata? Duk da cewa musuluimci ne ya basu yanci amma kuma musulmai ne suke qoqarin tauye hakkinn mata a cikin rayuwar auren suna yau da kullum.
Ba yadda za a yi a ce mace ta baro gidan iyayen ta domin tazo rayuwar aure da kai, kuma ka kuntata mata.
Ka sani a yayin da take neman barin gidansu, suna kewar rabuwa da iyayen ta, qannen ta, yayun ta, da danginta. Ta san da tana son su amma ta yarda ta biyon ka dan ku zauna ku raya sunnar ubangiji.
Mai yasa za ka zalumce ta? Wa jibi ne Malam Bahaushe ya tausayawa mace a cikin gidansa. Ya sani mace ba an kawo tab a ne a dalilin lokacin da yake da buqatarsa ya biya akan taba.
Ta na da ‘yancin a cikin gida kamar yarda wasu ma suke da yanci a cikin gida. Bauta da dawainiya a gida wannan mace tan a yi ne saboda ihsani na kyautatawa.
Idan za muyi Magana ta yadda Allah yake cewa; ku ciyar da matan ku ku tufatar dasu, ku zama ababen adalci a tsakanin su. Wajibi ne maza ku yi adalci a cikin zaman takewar aurarrakinku. Ku zama ababen koyi a rayuwar auren Manzan Allah da Matayen sa. Musgunawa da cin zarafin mace a rayuwar aure ko ba ma a rayuwar aure ba babu mai yi sai na mijin lalatacce.
Mu zamo ababen koyi a zaman takewar auren mu. Maza ku bada hakkinn mace da yake wuyanku ga matanku. Mata kuma ku kyautatwa mazajenku ta hanyar musu biyayya daixan gwargwado.