Ashraf Sanusi Lamido, ɗa ga tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa ya taba tambayar mahaifinsa a lokacin yana sarki, cewa yaushe ne zai ba shi mukamin sarautar gargajiya.
A hira da BBC kai tsaye a shafin Instagram, Ashraf ya ce da ya bukaci hakan sai mahaifinsa ya ce masa ya je ya ci gaba da karatu – sai wani lokaci a gaba za a duba wannan bukatar.
“Na aika wa Takawa [Sarki Muhammadu Sanusi II] sako ta WhatsApp cewa yaushe za a ba ni sarauta, sai ya ce mani in ci gaba da karatu”, in ji Ashraf.
Ya kuma bayyana cewa lokacin da aka nada mafaihinsa a matsayin Sarkin Kano an ce ma kannensu su daina yin Ingilishi a cikin gida su dinga magana da harshen Hausa.
Da aka tambaye shi ko yana da wani buri na mulkin siyasa, sai ya bayyana cewa ya fi son jama’a su duba cancantarsa a kan wani abu sannan sai ya duba yiwuwar neman wannan abun.
Ya kara da cewa “Idan shiga siyasa za ta sanya ni in kauce daga addinni, to ba zan shiga ba.”
Ashraf ya shawarci matasa su mayar da hankali wajen neman ilimi domin kada su bari a yaudare su ko kuma a jefa su cikin duhu.
Ya kuma yi kira ga matasa su yi kaffa-kaffa game da yadda suke amfani da shafukan sada zumunta, yana mai cewa ya kamata su rika amfani da su ta hanyar da ta kamata.