‘Yan wasan Liverpool sun nuna goyon bayan masu zanga-zanga a Amurka wadanda suke tur da hukumomi kan kisan da wani dan sandan kasar ya yi wa wani bakar fata George Floyd a Minneapolis.
Sun nuna goyon bayan ne ta hanyar dakatar da atisaye sanna suka sanya gwiwa daya a kasa a tsakiyar filin Anfield.
A hoton da aka yi wa ‘yan wasan Liverpool 29 a Anfield an rubuta cewar ”Hadin kai yana da karfi da kuma maudu’in ‘Rayuwar bakar fata mahimmiya ce”’.
An ce ‘yan wasan kungiyar ne suka bukaci yin hoton lokacin atisaye ranar Litinin.
‘Yan wasan tawagar Ingila Marcus Rashford da Jadon Sancho sun goyi bayan zanga-zangar da ake yi kan kyamar kashe George Floyd.
An fara zanga-zangar ne bayan da aka kashe Floyd wanda ba ya dauke da makami ranar 25 ga watan Mayu.
Wani dan sandan Minneapolis, Derek Chauvin ne ya tsare Floyd ya saka masa ankwa a hannu ya kuma kwantar da shi a kasa ya danne masa wuya da gwiwar kafa kusan minti tara har sai da ya mutu.
Ana tuhumar Chauvin da laifin kisa an kuma kore shi daga aikin dan sanda.