Ariziki Daka Allah ne Kuma shikeba Wanda yaso alokacin dayaso.
Karanta wanan labarin don fahimtar abunda Ake nufi.
Bayan kwashe fiye da shekaru 30 ta na aikin kula da fasinjojin jirgin sama, Sandy Stein, mai shekaru 65 a yanzu ta yi kudi.
Stein na da shekaru 53 lokacin da ta kirkiro wata sarkar adana makullai wacce ake makalawa a jikin jaka, ta yadda ba za’a sha wuyar laluben makullai a cikin jaka ba.
A wannan shekarar ta sai mota mai tsada, ta dauki mutane aiki kuma ta yi cinikin fiye da dala miliyan hudu.
Wannan rayuwa ce mai dadi ga mutane da dama. Sai dai kuma ga mamakin Stein, babban abinda wannan arziki ya jawo mata shi ne kadaici.
Mijinta ya sake ta saboda a baya shi yake daukar nauyin komai a gidan, don haka ya fara kyashin arzikin da Stein ta samu. Alakarta da kawayenta ma ta shiga tsaka-mai-wuya.
Tace “kawayena sun shiga hassada kuma sun nuna min kyashi.”
Kodayake mafi yawan mutane na ci gaba da fatan yin kudi, masu kudin na cewa su na fama da kadaici kuma rayuwarsu tafi ba da sha’awa ga mai kallonsu daga nesa.
Idan mutum ya yi kudin dare daya, tasirin hakan na taba dukkan sassan rayuwarsa,” in ji Dr. Stephen Godlbart, daya daga cikin wadanda su ka kafa kamfanin Money, Meaning & Choices Institute, mai bai wa masu kudi shawarwari kan yadda zasu tafiyar da rayuwarsu. “Ya kan jawo tsananin bacin rai da takaici ga wasu mutanen.”
Ya kara da cewa masu kudin dare daya kan samu kansu cikin rudani tare da kadaici da bacin rai.
Namu ya samu
Da yawanmu mun shafe shekaru da dama muna burin samun arziki. Amma da zarar kudin sun samu sai mu gano cewa ba mu shiryawa sauye-sauyen da zamu fuskanta daga mutanen da ke kewaye da mu ba.
Da ma dai wannan ba wani batu ba ne da mu kan bata lokutanmu mu na tunani a kai. Don haka idan abokai su ka fara janye jiki (ko kuma su ka kara matsarmu) sannan iyalanmu su ka fara shiga harkokinmu wadanda ba su saba shiga ba a baya, sai abin ya bamu mamaki.
A bangare guda, kudi kan sauya mutane. Wani lokacin masu kudin dare daya, ku sun sani ko ba su sani ba, kan sauya dabi’unsu ta hanyar almubazzaranci ko daina wasu abubuwa da su ke yi a baya, wadanda za su janyo musu rabuwa da tsofaffin abokansu, in ji Megan Ford, shugabar kungiyar masu bada shawara kan harkokin kudi ta Amurka.
Ta kara da cewa “abokai ba zasu su so su sauya kansu domin dacewa da sabon tsarin da ka zo da shi ba”, don haka sai su janye daga gare ka, abinda zai kara maka takaici.
Samun kan ‘yan uwa da abokan arziki shi ne yafi wahalarwa. Mutanen nesa kan yi kokarin su biya bukatar masu sabon kudi, amma ‘yan uwa da abokai su ne ke kokarin kara nanike wa wanda su ke ganin yanzu ya zama gwarzo, in ji Goldbart.
Kuma ya zaka yi idan ‘yan uwa da abokai su ka fara mai da kai wani dabam? Mafi yawanmu za mu fara zargi ne. Ina wadannan ‘yan uwan da abokan lokacin da ka ke ta gwagwarmayar neman arzikin? Hakan na sa kai ma ka ja jiki ka takaita yawan abokanka, saboda ba ka tabbacin waye ke kokarin kusantarka, kawai don ‘ka shigo gari’.
Wannan tunanin ba ya kaucewa idan kudin na ka su ka zauna. Gano wanda ke neman abotar gaske da kai na da matukar wahala kuma duk lokacin da ka yi kuskuren amincewa da wani, daga baya kuma ka gano cewa kudinka ya biyo, sai ka kara gujewa mutane, a cewar Ford.
More arzikinka
Wadanda su ka yi kudin dare daya sun ce sababbin damarmakin da su ke samu na kara musu kadaici. Stephan Goss mai shekaru 28, dan asalin Switzerland ne da ya koma San Diego ta kasar Amurka da zama. Ya ce tilas ta sa shi neman sababbin abokan da suke da irin damar da yake da ita.
“Mafi yawan mutane ba zasu iya cewa bari mu tafi Mexico hutu a gobe ba. Don haka sai ya yawo da abokanka na da ya gagara saboda su ba zasu iya barin wuraren ayyukansu ba,” in ji Goss, wanda ya kafa Zeeto Media, kamfanin da ya ke bai wa masu wallafa a intanet damar sayar da bayanansu.
Duk da yake Goss bai yi watsi da abokan da ya yi lokacin tasowarsa a Switzerland da abokansa na jami’a ba, a mafi yawan lokuta ya na rayuwa ne tare da masu kudi ‘yan uwansa da ke da damar yin abubuwan da ya ke sha’awar yi.
Koda yake ita Stein ba ta ga haka, masana sun ce tasirin kudin dare daya yafi sauki akan tsofaffi, wadanda su ka jima su na aiki, saboda makusantansu sun fi sa ran dama zasu samu kudi, a cewar Goldbart.
Har Yanzu dai Stein ba ta daidaita sabanin da ta samu da ‘yan uwa da kawayenta ba. Sai dai yanzu ta na da kyakkyawar alaka da manyan ma’aikatanta guda biyar, wadanda tace ta gano ‘yan amana ne.
Haka kuma yanzu ta fahimci kawayen da su ka yi zaman gaskiya da ita lokacin da ta ke aikin jirgin sama kuma ta na yi musu kyauta sosai. Daga cikin abinda yafi mata dadi shi ne daukar wata abokiyar aikinta da ta yi zuwa yawon kallon dabbar ‘bear’ din da ke rayuwa cikin kankara
Ta ce; “Na yi matukar farin ciki da na samu damar yin haka.
[covid-data]