A yayin da a baya-bayan nan matsalar rashin tsaro ta sake tabarbarewa a fadin kasar nan musamman Arewacin Najeriya, wani bincike ya nuna rayukan fiye da mutum 500 sun salwanta a cikin watanni uku kacal.
Binciken manema labarai na jaridar Daily Trust ya gano cewa, rashin tsaro ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 500 cikin wasu jihohi 10 na Najeriya a tsawon watanni uku da shude.
Mutanen da rayukansu suka salwanta sun hadar da fararen hula, jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai a sanadiyar rikici kabilanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma tayar da kayar baya.
Yankunan kasar da wannan mummunan lamari ya dugunzuma sun kasance yankin Arewa ta Tsakiya, Arewa ta Gabas, da kuma Arewa ta Yamma.
Jihohin 10 da suke neman zaman lafiya da kwanciyar hankali ruwa a jallo sun hadar da; Katsina, Kaduna, Taraba, Zamfara, Niger, Benue, Sokoto, Borno, Yobe da kuma Adamawa.
Wannan lamari wani dori ne a kan wahalhalu da matsi na tattalin arziki da ke fuskantar miliyoyin mutane a yankunan a yayin da annobar cutar korona ta ke ci gaba da tsananta.
Ana ci gaba da samun banbance-banbance na tunkarar wannan mummunan lamari a tsakanin gwamnoni da jami’an tsaro a yankunan da zaman lafiya ya dade da yin layar zana.
Sai dai ko shakka babu al’umma da mazauna yankunan wanda su kadai suka san irin hatsarin da suke ciki, babu abin da suke bukata a halin yanzu face rokon a kawo musu dauki kafin wataran a waye gari babu su gaba daya a doron kasa.
Dubban dangi sun rasa ‘yan uwa da makusanta a yayin da ba dare ba rana rashin tsaro yake ci gaba da kara yawan zawarawa da kuma marayu, wanda hakan yake kara tsananta katutu na talauci da sauran kalubale na rayuwa.
Haka kuma wani hasashe ya nuna sakamakon rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, kimanin mutane 8, 000 sun kwanta dama a shekaru goman da suka gabata.[
[covid-data]