Mazauna garin Ruwan Tofa cikin ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun auka cikin tashin hankali bayan ‘yan fashin daji sun yi wa yankinsu tsinke tun a ƙarshen makon jiya.
Bayanan baya-bayan nan daga jihar na nuna cewa akalla mutum 21 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon harin ‘yan fashin daji a ranar Asabar.
Mutanen garin sun ce mahara fiye da 200 ne a kan babura suka auka wa garin tare da buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi lokacin da suka yi yunkurin artabu da su.
Wani mutumin Ruwan Tofa ya shaida wa BBC cewa daga cikin mutanen da aka kashe har da wata mace ɗaya, da kuma namiji 20, yayin da aka jikkata ƙarin mutum goma sha biyar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara dai ta ce zuwa yanzu ta tabbatar da mutuwar mutum goma ne sakamakon wannan hari na yammacin Asabar
Shi dai wannan shaida ya ce mutanen da aka jkkata suna cikin mawuyacin hali, yayin da mafi yawansu ke can kwance a babban asibitin yankin.
Haka zalika, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da dukiyar jama’a ciki har da tumaki da shanu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce baya ga mutum 10 da suka tabbatar an kashe, sun samu rahotannin gano ƙarin waɗanda suka mutu wasunsu bayan an su asibiti.
Ya ce tuni aka tura ƙarin jami’an tsaro na haɗin gwiwar sojoji da ‘yan sanda zuwa garin Binɗim don shawo kan lamarin.
Ko a farkon wannan wata ma sai da wasu ‘yan fashin daji suka kashe fiye da mutum 70 a wasu hare-hare da suka kai ƙauyuka cikin kwana biyu.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun fara far wa mutanen kauyukan ne a ranar Talata inda suka kashe mutum 15.
Kafin su sake far wa mutane yayin da ake jana’izar waɗanda aka kashe inda maharan suka kashe mutum 50.
Abin ya faru ne a kauyukan Gidan Ƙane da Tungar Mawa da ‘Yar Gada da kuma wasu kauyuka da ke yankin.