Ministan harakokin waje Mohammad Javad Zarif ya ce Iran a shirye ta ke ta tattauna da Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa kan barazanar tsaro.
A yayin da yake magana a wani shirin kafar talabijin ta (IRTV2), Zarif ya yi tayin tattaunawa ga ƙasashe takwas da suka haɗa da Iran da Saudiyya da Bahrain da Iraƙi.
“A shirye muke mu hau teburin tattaunawa da juna.”
Ya kuma ce kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na da ƴancin samar da hurumin tattaunawa kamar matakin da aka ɗauka da ya kawo tsagaita buɗa wuta tsakanin Iran da Iraƙi a 1988.
Sai dai kuma a cikin kalamansa, Mista Zarif ya soki Saudiyya musamman Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman kan yaƙin da ƙasar ke ci gaba da jagoranta a Yemen.