Indai Zamani Sanata Sai Ancutar Da Al’umma Allah Ka Rabani Da Zama Sanata
Duk Shugaba na kwarai Babban burin sa shine samarwa alummar sa zaman lafiya, kwanciyar hankali da kare musu dukiyar su da rayukansu- Inji Hon. Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila Ofr.
Hon. Kawu Sumaila yakara dacewa” Idan har sai an cutar da mutanen da suka bani kuri’arsu, mutanen da suka nunamin soyayyar su da damkamin amanar su, ko kuma anbaiwa matasa sunsha miyagun kwayoyi da sara-suka sannan ne zan zama Sanata Allah karabani da zama sanata.
Duk mutumin da burinsa zubar da jinin mutane tom yasani karshen yazo.ED
idan muka tuna baya a shekarar 2015, tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan yana kan kujerar mulkin Nijeriya shine keda ikon juya kowacce ma’aikata da hukumomi amma akace yafadi zabe kuma ya aminta ya fadi yabayar da mulki ya sauka, balle kai da baka kaishi matsayi ba, kace saika tursasa mutane saika tayar da hankalin mutane kuma a matsayin kana kiran kanka musulmi to bazamuce komai ba saidai muce Allah ya sauwake.
Adalci da bayyana gaskiya da amana ba’a samunsu a gun mutumin da bana kwarai ba, duk sanda kake tunanin yin zalunci ka tuna wataran wanda kake zaluntar nan Allah yana kallonsa kuma tabbas wataran zai bashi damar da tafi taka, domin zalunci baya dorewa kuma bazai dauwama a tare da wanda akewa ba.
Mutanen da suka zabe ka, kuma kake wakilta, ace kaine zaka baiwa ‘ya ‘yansu muggan makamai da miyagun kwayoyi domin kawai wata bukatar ka.
Ina kara kira ga Al’umma musamman matasan mu, yakamata mu farka mugane mutanen da basu damu da rayuwarmu ba, da zaman lafiyar mu ba, sunfi son bukatar kansu akan ta alumma koda kuwa al’umma zasu shiga kangin rayuwa, da kada mukara yarda dasu wakilce mu adukkan gurabe