Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.
A makon da ya gabata ne dai labari ya bulla na mutuwar wata budurwa a wani coci da ke jami’ar jihar Benin, wadda alamu suka nuna cewa ta mutu ne bayan da wasu maza suka yi mata fyade.
Wannan lamari ya haifar da zanga-zanga da kiraye-kiraye na ganin an yi adalci kan faruwar lamarin.
Ko a shafukan sada zumunta mutane sun yi ta alla-wadai da karuwar fyade a kasar tare da neman gwamnati ta dau kwararan matakan kawo karshen wannan bala’i.
Shugabar kungiyar mata ta Women in Leadership Initiative a Najeriya, Maryam Baba Mohammed ta shaidawa BBC cewa fyade ba a kan kananan mata kawai ya tsaya ba har da yara maza.
Maryam na daya daga cikin masu hankoron ganin an kwato wa wadanda aka yi wa fyade hakkinsu, kuma ta ce sun sha magana da jawo kan hankali mutane kan wannan mumunan ta’adda amma ba a yanke musu hukunci.
Maryam ta ce ”mutane basa magana su kan yi shiru da sunan kunya ko kare mutunci ko sunan yarinya, wannan dalili ya sa ba a daukan hukunci kuma masu aikata fyade ba sa daina wa”.
”Yanzu shafukan sada zumunta na da karfi don haka a wannan lokacin kiran namu zai yi tasiri domin an tashi haikan don ganin an shawo kan matsalar”
Mai fafutikar ta danganta rashin daukan hukunci da haifar da karuwar fyade kan kananan yara a Najeriya. Sannan ta ce a da ana tunanin mata zalla kawai ake yiwa fyade amma a yanzu maza musamman kanana na cikin hadari su ma.
”Ba su mu bari wannan maganar ya kwanta ba, samu bi kadi mu tabbatar an kwantowa wandanda aka keta wa hakkinsu”
Yara da aka yi wa fyade za ka ga idonsu ya bude ga rashin natsuwa da tsoro a wasu lokutan, in ji Maryam.
Gwamnatin tarayya dai tuni ta ce ta bayar da umurnin yin bincike da zakulo masu hannu kan lamarin.