Mai girma Kwamishinan ma’aikatar kula da kasafin kudi da tsare tsaren tartalin arziki na Jihar Katsina Hon. Faruk Jobe ya yaba kan yadda yaga Al’umma maza da mata suka fito don sabunta rajista da katinsu na zama ‘Yan jam’iyyar Apc a cikin mazabar shi.
Hon. Jobe ya yi wannan yabo ne lokacin da yaje mazabar shi ta (KOFAR FADA)Kankara A&B ward a safiyar yau Alhamis 11/02/2021 don ya sabunta rajista da katin shi na zama Dan jam’iyyar Apc, da uwar jam’iyyar Apc ta kasa ta bada umurnin sabuntawa ga duk Dan jam’iyyar da kuma mai sha’awar shiga cikin jam’iyyar.
A karshe Kwamishinan ya jawo hankalin masu gudanar da aikin sabunta rajistar da katin zama Dan jam’iyyar, dasu tabbatar sunyi ma duk wanda yazo ya nuna sha’awar shi ta shiga cikin jam’iyyar Apc, domin jam’iyyar Apc ta kowa ce da wanda ya dade cikinta da wanda ya shigota a yau duk daya ne, babu wanda yafi wani. Ya yi addu’ar Allah yasa a gama wannan aiki lafiya.