Wasu makiyaya da su ka tsere daga harin mutanen yankin kudu sun fara dawowa jihohin Arewa Kimanin makiyaya sama da 4,000 ne su ka tattara nasu-ya-nasu su ka dawo wani yankin jihar Kaduna. Sun bayyana cewa da yawan su sun rasa komai, su na kuma bukatar abinci da abubuwan rayuwa na yau da kullum sakamakon umarnin fatattakar makiyaya ma su aikata laifuka a wasu jihohin kudu, kimanin makiyaya 4,000 sun bar jihohin kudu zuwa Kaduna, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito. An ce makiyayan tun makon da ya gabata su na dawowa zuwa garin Labduga, karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.
Wani jami’in Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Hussaini Abdullahi ya ce, ya zuwa yanzu sun tabbatar da dawowar kimanin makiyaya dubu hudu, kuma har yanzu wasu suna nan tafe. Ya kuma ce hukumar sa da wata kungiya mai zaman kanta, mai suna ‘Early Recovery Initiative’ su na gudanar da binciken kwa-kwaf ga makiyayan da su ka tsere don neman taimako.
“Ba mu tanadar musu da wani sansani na musamman ba, su na zama ne cikin al’ummar da ta sauke su, su na samun taimakon gaggawa daga dangi da kuma wasu mutanen gari.
“Mafi yawan su sun rasa abinda su ke samu na rayuwa, sun gaya mana cewa su na bukatar abinci da abubuwan da ba abinci ba cikin gaggawa, amma kuma mun lura cewa su na fama da matsalar halayyar dan adam kuma a saboda haka, su na bukatar shawarwari.
“Nan ba da dadewa ba za mu ziyarce su kuma mu gudanar da bincike kan halin da su ke ciki don ganin inda za mu taimaka musu.”
Shi ma da ya ke magana, Daraktan yaxa Labarai, reshen jihar Kaduna na kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), Ibrahim Bayero ya bayyana cewa hakika halin da su ke ciki abin tausayi ne.
“Mun fara tattara mambobin mu don ganin yadda za mu taimaka musu. Kamar yadda mu ke tsammanin karin su, ” inji shi.
Hussaini Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a ofishin sa, ya ce mataimakin sa wanda ke wakiltar Ondo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice, zai gabatar da kudiri kan batun.