Dalilin da yasa Zulum ya jagoranci Dattawan Borno, Yobe don ganawa da Buhari
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Talata ya jagoranci wata babbar tawaga ta dattawa da masu ruwa da tsaki daga jihohin Borno da Yobe zuwa ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa.
Tawagar na da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, tsoffin gwamnonin jihar Borno, Ashiek Jarma da Sanata Kashim Shettima, Shehu na Borno, Alhaji Dr. Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi, da Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa.
An sanar da cewa, wannan babban taron ya maida hankali ne kan dorewar nasarorin da sojoji suka samu a yakin da suke da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Har ila yau, tattaunawar ta tattauna batun sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar zuwa garuruwa da kauyukan da ke da aminci, gyara da sake gina manyan titunan Tarayyar a jihohin Borno da Yobe, da sauransu.
Zulum, yayin zantawa da manema labarai bayan ganawar, ya ce Shugaban ya ba da tabbacin dorewar farmakin sojoji a ayyukan da ke gudana a Borno da sauran sassan arewa maso gabas.