Shugaban Majalisar Malamai ta Saudiyya kuma Babban Mai Fatawa, Abdul Aziz Al Asheikh ya ce ya halatta mutane su yi Sallar Idi a gidajensu a irin wannan lokaci na annobar korona.
Sallar Idi ta ƙunshi raka’a biyu ce tare da yin kabbara shida a raka’ar farko sannan a yi kabbara biyar a raka’a ta biyu.
Da yake tattauanwa da haɗin gwiwar jaridun Okaz da Saudi Gazette, Al Asheikh ya ƙara da cewa za a iya bayar da zakkar fidda kai ta hanyar ƙungiyoyin bayar da agaji idan an aminta da su.
Shi ma Sheikh Abdul Salam Abdullah Al-Sulaiman, wani mamba a kwamitin fatawa, ya ce za a iya yin Sallar Idi a jam’i ko kuma mutum ɗaya.
Sheikh Al-Sulaiman ya bayar da misali da sahabin Annabi mai suna Anas Bin Malik, inda ya ce yayin da yake gidansa a Zawiya bai samu inda ake yin jam’in Idi ba sai ya yi sallar a gida da iyalansa da kuma mai yi masa hidima Abdullah Bin Abi Otba.
Saudiyya ta ɗauki matakin hana Umara da dakatar da shirye-shiryen aikin Hajji sakamakon ɓarkewar annobar korona.
Kazalika an dakatar da dubban jama’a shiga Masallatan Haramai biyu domin yoin sallar asham ko tarawihi ta azumimn Ramadana, inda ‘yan ƙalilan ne kawai ke gudanar da sallolin.
Alƙaluman Jami’ar Johns Hopkins sun nuna cewa mutum 57,345 ne suka harbu da cutar korona a Saudiyya, 320 sun mutu da kuma 28,748 da suka warke.
[covid-data]