Tsohon kwamishinan jihar Kano da aka sallama daga aiki bisa zargin ya yi murnar mutuwar tsohon shugaban fadar gwamnatin Najeriya, Injiniya Mu’az Magaji ya ce ya yi nadama game da halin da ya shiga.
Ya ce akwai darussa da yawa da ya koya, wasu na siyasa, wasu na zamantakewa, wasu na mu’amala, wani (darasin ma) tsakanina da Mahalicci.
Injiniya Mu’az Magaji ya fada a zantawarsa ta wayar tarho da BBC daga cibiyar masu korona da yake kwance cewa: “Ai duk dan’adam idan ya shiga wani hali to ya kamata ya ja baya kuma ya koyi darasi”.
A ranar 7 ga watan Mayu ne, tsohon kwamishinan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwajin korona da aka yi masa ya fito har ma ya nuna cewa shi ma ya kamu da cutar.
Lamarin ya zo ne kwana 20 bayan sauke shi daga kan mukaminsa bisa zargin yin murna da rasuwar Malam Abba Kyari. Ko da yake ya sha musun cewa Ban yi murnar rasuwar Abba Kyari ba.
Mu’az Magaji ya nanata cewa zargin da aka yi masa duk rashin fahimta ne. Ya ce “Wanne musulmi ne zai yi murnar mutuwar wani dan’adam, ba ma dan’uwansa musulmi ba?”
“Abin da na yi magana a kai shi ne wato shi Abba Kyari a matsayinsa na babban ma’aikaci(n gwamnati) kuma Allah Ubangiji Ya dau ransa a cikin irin wannan hali na annoba kamar yadda Sheikh Pantami ya fada a lokacin jana’izarsa, to duk wanda ya mutu a cikin wannan hali ya yi dace ya yi shahada,” in ji maras lafiyan.
Ya ce wannan kalami ya yi sai wasu ke tunanin: “kamar ina murna wani ya rasu….Wannan ba daidai ba ne”.
Da aka tambaye shi ko me ya sa ya yi ta jera sakwanni a ranar da aka yi wannan rasuwa? Tsohon kwamishinan ya ce matsalolin da ke tattare da ofishin “a kansu ne muke ta ba da shawara”.
A cewarsa: “Mun dade muna bayani a kan tsari na dimokradiyya, yana da kyau ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa (bai kamata a ce) karfinsa ya zo ya fi na ministoci da sanatoci da ‘yan majalisar da jama’a suka zaba ba”.
Ya ce cikin halin ranga-ranga aka kai shi asibiti bayan ya kamu da cutar, inda ya yi ta amai da gudawa da kuma zazzabi.
Mu’az Magaji ya ce ya wayi gari da ganin gawa a kusa da shi ya fi sau biyu bayan kai shi sashen kula da masu matsananciyar jinya sakamakon cutar korona da ta yi ajalin Malam Abba Kyari.
Ya ce amma yanzu ya samu sauki don kuwa an fito da shi daga sashen masu matsananciyar jinya kuma yana ci gaba da murmurewa.
[covid-data]