Cutar korona ta janyo koma-baya cikin al’amura da dama a rayuwar dan’adam ta yau, kama daga fannin tattalin arziki da ilimi da lafiya da sauran bangarori.
A bangaren ilimi, an dakatar da zuwa makaranta a kusan duk fadin duniya, haka abin yake a Najeriya, kasa mafi yawan jama’a cikin nahiyar da ke yankin yammacin Afirka.
A arewacin Najeriya cutar ta janyo dakatar da makarantun allo wadanda su ne matattarar almajirai da akan tura karatu daga garuruwansu lamarin da kan sanya su yawon bara a kasar.
Gwamnatoci a arewacin kasar, sun ja ɗamarar mayar da duk wani almajiri da ke cikin jihohinsu zuwa ainihin mahaifarsa.
Wannan ya zo ne sakamakon wata yarjejeniya da gwamnonin suka cimma inda suka dogara da fargabar cewa annobar korona ta fi barazanar yaduwa a wurare masu cunkoso da karancin tsafta kamar makarantun allo.
Hakan ya sa aka bai wa masu unguwanni da sauran shugabannin al’umma umarnin shaida wa malaman tsangaya yunkurin gwamnatoci na mayar da wadannan almajirai zuwa jihohinsu.
Matakin tamkar a iya cewa an yi sara ne daidai kan gaba, da yawan jihohin sun washi tsarin karatun na almajiranci kuma suna ta neman hanyar da za su samu su dakatar da shi, ba tare da fuskantar zazzafar adawa ko tirjiya ba.
Alaramma Bayero Badamasi na cikin malaman tsangayar da suka mayar da almajiransu tun farkon samun wannan umarni, ya ce yana da almajirai kimanin 50 da ke karatu a makarantarsa.
“Lokacin da na mayar da waɗannan yara gida babu masu dauke da korona biyar a Kano, kuma na ga kaskanci wajen mayar da su gidan.
Yaran sun fito daga jihohin Bauchi na Katsina da Yobe ne, da farko wani gardi na umarta ya mayar da su, sai aka hana su shiga Bauchi aka dawo da shi. Karshe dai da kaina na mayar da su,” in ji shi
Mabanbantan ra’ayi kan Almajir an ci
An ta samun bambantan ra’ayoyi da fahimta kan wannan tsari na tsangaya wanda ke samar da almajirai a arewacin Najeriya.
Farfesa Ibrahim Maqary shi ne limamin babban masallacin birnin tarayyar Abuja a Najeriya, ya ce “Gwamnati ba za ta iya ɗaukar nauyin makarantun tsangaya ba, tsarin da ta shigo da shi na ilimin zamani ma ta gaza tafiyar da shi yadda ya kamata,
Don haka, jiran gwamnati a wannan bangare ta yi wani abu yaudarar kai ne.”
Karatun addini ba don neman kudi ake yin sa kamar takwaransa na boko ba, don haka tallafi har kullum shi ke rike tsarin,” in ji Farfesa Maqary.
A wajen Farfesa Maqary da za a samar da kudaden waƙafi (kudaden da masu kudi ke bayar wa don taimakon addini) to za a iya tallafawa tsarin karatun tsangaya.
Tun a 2019, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ja kunnen mahaifan da ke tura ‘ya’yansu almajiranci ko kuma bara maimakon neman ilmi, inda har ya ba da umarnin cewa a kama duk wani yaron da aka gani tare da bibiyar mahaifansa, a kama su baki ɗaya.
Shi ma tsohon sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya yi ta faɗi-tashin ganin an yi wa tsarin karatun tsangaya kwaskwarima, ta yadda za a haramta sakin yara barkatai a kan tituna, inda kuma har sukan fada hannun wasu miyagun mutane da kan aikata laifuka marasa kyau da su.
Ko a ina dai ba a ƙirga waɗannan almajirai da kuma tsarin karatunsu a matsayin ilimi, domin ko yaushe Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya tashi fitar da alkalunman yaran da ba sa zuwa makaranta yakan sanya jihohin arewacin Najeriya inda aka fi gudanar da irin wannan tsari, gaba-gaba.
Lamarin da ke ci wa mutanen arewaci da kuma gwamnatocin yankin tuwo a kwarya.
Almajirci a jiya
Babu wani bambanci tsakanin almajiranci a jiya da kuma yau, yadda ake kai yaro “Gabas” daga shi sai akwatunsa a baya, yau ma haka abin yake, illa iyaka dai maimakon Gabas, yanzu an fantsama ko’ina ana kai yara.
Kuma wani abu da aka lura da shi a wannan zamani shi ne iyaye na kai yaransu almajiranci ne domin guje wa daukar nauyin da ke kawunansu da kuma talauci,” In ji Alaramma Bayero Badamasi.
A zamanin baya ba a barin almajirai su je bara kan tituna ko kan mahadar titi. kusan kowanne yaro na da uwar gidan da yake yi wa aiki wadda a wurinta yake samun abinci kila ma har sau uku a rana.
A ranakun Alhamis da Juma’a, almajiran kan wanke allo kuma su yi sukola (wanki).
“Wani ma uwar gidansa ce ke masa aure idan girma ya zo masa rayuwa ta yi nisa,” in ji Alaramma.
Almajiranci a yau
Yara da yawa ba sa samun kulawar da ta dace daga malamansu da kuma iyayensu, a lokuta da dama wasu bata-gari na amfani da irin wadannan damarmaki wajen cin zarafi da tozarta yaran.
A bangaren Malamai in ji Alaramma Badamasi “Muna dauko yaran da suka fi karfin kulawar mu, sai ka ga malami bai san adadin almajiransa ba balle kuma sanin sunayensu daya bayan daya.
Alaramma Bayero Badamasi ya ce a bangaren iyaye kuwa, talauci da kuma kin daukar nauyin da addini ya dora musu na daga cikin abubuwan da ke sanya su kawar da yaran daga gabansu”.
Wannan na cikin dalilan da masu rajin kare hakkin dan adam ke kafa hujja da su wajen ganin an daina kai wadannan yara nesa da iyayensu.
Kuma malaman tsangaya da yawa a yanzu haka na ikirarin cewa, mafi yawan yaran da ake kamawa a tituna ba almajiran tsangayoyinsu ba ne.
Mayar da almajirai gida
Cikin watan Afirlun da ya gabata ne, gamayyar gwamnoni jihohin arewacin Najeriya 19, ta yi wani taro kan hanyar mayar da almajirai gida a wani mataki na dakile yaduwar cutar korona a yankunansu.
Miliyoyin almajirai aka ambato gamayyar na shirin mayar wa jihohinsu na asali.
Iyaye da yawa a arewacin Najeriya na tura yaransu ciki har da kananan yara ‘yan kasa da shekara shida, zuwa makarantun allo domin sauke Al Kur’ani mai tsarki.
Ana bayyana damuwa kan makomar yaran, musamman yanzu da cutar korona ke ci gaba da bazuwa a jihohin arewancin Najeriya.
A 2014, wani kwamitin wasu fitattun mutane da suka shafe wata takwas suna yi wa gwamnonin arewa nazari kan wasu matsaloli musamman na barace-barace, sun gabatar da rahoto kan yadda za a magance su.
Sai dai sama da shekara biyar da mika wa gwamnonin wannan rahoto, za a iya cewa ba a ga wani sauyi ba.
‘ Raguwar dabara ‘
Alaramma Badamasi Bayero da tuni ya mayar da almajiransa hannun iyayensu a jihohin da suka fito ya ce ” wannan matakin bonono ne wato rufe kofa da barawo.
Maimakon kawo karshen cutar sai dai ma kara yada ta zuwa kauyukan da babu ita, wadanda ba su da asibitoci a kusa da su, kauyukan da magani ma ba a sayarwa,” in ji Alaramma.
Abu na biyu kuma “wasu yaran ba su da iyaye, malamin shi ne uwa shi ne ubansu – kuma makarantar nan ne danginsu, idan ka mayar da su kauyukansu, to su koma hannun wa?
Akwai fargabar kada yaran nan su zama barazana ga zaman lafiyar yankin arewa da kuma kasa baki daya saboda za su zama ba su da mafadi.” A cewarsa.
A baya, mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya ce, gwamnatin Muhammadu Buhari na son ganin ta tsaftace harkar almajiranci a arewacin kasar.
Ta yadda za a zauna da masu ruwa da tsaki kan al’amarin domin lalubo bakin zare.
Wannan batun dai ya ja hankalin ‘yan Najeriya a wancan lokacin, inda a wata sanarwa da Malam Garba Shehun ya fitar, Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dauki matakin hana bara amma fa ba a nan kusa ba.
Kafin sanarwar, Shugaba Buhari ya nanata aniyarsa ta ganin dukkanin yara ‘yan Najeriya sun samu ilimin da ya dace, inda ya ce zai dauki matakan magance abubuwan da ke hana kananan yara zuwa makaranta.
Sai dai har yanzu shiru kake ji babu wani mataki daga gwamnatin tarayyar Najeriya.
Batun Almajiranci a arewacin Najeriya shi ne wani batu da ya fi janyo ce-ce-ku-ce musamman kan yadda za a gyara tsarin domin dacewa da zamani da ma yadda ake gudanar da irin tsarin a wasu kasashen musulmi da suka ci gaba a duniya.
Wasu dai sun yin kira a haramta bara a wajen kananan yara, inda wasu kuma ke cewa ba haramta ta ya kamata a yi ba illa kawai a sake wa tsarin sabon fasali.
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya fito da wani tsari na sanya almajirai cikin wani dunkulallen tsarin karatun zamani inda aka gina makarantu domin koya musu Alqur’ani hade da na boko a wasu jihohin arewa.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko annobar korona za ta yi sanadin yi wa karatun almajiranci garanbawul ko kuma kawo karshen al’amarin bisa dogaro da yadda wasu jihohi suka fatattaki almajiran zuwa jihohin da suka fito.
[covid-data]