Daag: Dr Aliyu Ibrahim Kankara
Gaisuwa da fatan alheri, tare da fatan Mai martaba ya kasance a cikin lafiya.
Allah Ya sanya muna daga cikin ‘yantattun bayin Sa a wannan babban wata na azumi mai albarka, mai alfarma. Allah Shi taimaki Mai martaba, ina kira ga wannan babbar masarauta ta ka da ta gaggauta xaukar mataki akan wasu samari matasa a cikin birnin Katsina da ba su yin azumi.
Ko’ina ka duba a cikin birni, ba ma dai yankunan unguwannin Rahamawa da Qofar ‘Yanxaka da bakin rawul na babbar tasahr mota ta gwamnati, zuwa hanyar Batsari, da dai wuraren da ake hada-hadar sayar da kayan masarufi, galiban matasan da za ka gani a wuraren, to wallahi ba su yin azumi.
Qiriqiri, saboda ma yi ma Allah (SWA) gatse da gadara, za ka ga sun riqe sigari ko wiwi suna sha, a cikin bainar mutane. Wai su su nuna ma mutane cewa su tabbatattu ne, marasa kunya.
A sani na ne, qasashen Larabawa da makamantan su, gwamnatocin su su kan naxa jami’an gwamnati su rinqa zagayawa a kowanne lungu ko saqo na qasashen su su kamo waxanda ba su yin azumi.
Sabili da shi kan shi rashin yin azumin, matuqar dai babu larura, to babban bala’i ne. Domin haqqin Allah ne ake karyawa. Rashin azumin shi kan sa na jawo ma al’umma bala’o’i da tashe-tashen hankulla iri-iri.
Kuma wannan alhaki ne da ya rataya akan hukumomi, su kasa su tsare.
A Saudiyya, duk wanda aka kama ba ya yin azumi, to za a kai shi a kulle shi, sai bayan an taso sallahr Idi ranar sallah sannan a sako shi. Gobe ma ya qara.
To amma har yanzu ni ban ga hukumomin Nijeriya na yin wannan hukuncin ba. Lokaci ya yi da yakamata a yi wani abu don a ceto al’ummar mu daga ida lalacewa kwatakwata. Tilasta ma samari matasa su rinqa yin azumin za ya sanya a samu sauqin shawo kawunan su, su zamana masu amfani ga al’umma can gaba.
Sannan kuma su samu matakin samin ilimin addini. Tun kafin azumi, ya zuwa satin da ya gabata, lokacin xarayi ‘yan ta’adda, tsinannu waxanda Allah Ya tsine ma albarka, kafirai, masu fashi da makami suka tarwatsa wasu
qauyuka na gefen Katsina daga yamma, kamar su ‘Yan gero da Bakiyawa da qauyukan da ke yammacin Babbar Ruga, da sauran su.
Wanda har ya zuwa yau xin nan mutane na nan maza da mata da yara qanana, gami da dabbobin su suna ta kwararowa cikin birnin Katsina domin samun mafaka da gudun hijira. Wasun su na nan sun yi sansani a bakin gari, da fuskar yamma (a kan hanyar Batsari), wasu kuma na nan cikin unguwannin gefen gari, kamar su Rahamawa.
To, Allah Shi taimaki Sarki, su kan su masu gudun hijirar, daga cikin su akwai varayi waxanda ba su yin azumi. Gasu manya ne, qatti, amma na banza. Da gari ya waye za su tafi can bakin daji daidai babbar kwaltar da ta zagaye Katsina (Ring Road) su yi sansani.
Ba abin da suke yi sai shaye-shayen tabar ibilis watau wiwi da sigari, da kuma caca ko karta.
Da mangariba kuma su dawo cikin unguwanni suna bara, a matsayin wai sun yi azumi. Sannan kuma da dare su bi gida-gida suna yi ma mutane sata.
Ni kai na an shiga cikin zauren abokina a unguwar Rahamawa an sace masa mashin, a satin da ya gabata. To waxannan ba ‘yan gudun hijira ba ne na haqiqa, dama can varayi ne.
Ina kira ga masarautar Katsina da ta sa ido ta kula sosai akan sha’anin aiwatar da addini da sauke nauyin Ubanguji (SWA) da mazauna birni ke yi.
An san cewa al’umma ta gurvace, kuma an san cewa gyaran ta na daga Ubangiji. Idan mun gyara halayen mu, to Allah Za Ya gayar mu, sannan Ya gyara mana shuwagabannin mu. Kuma na san cewa shi dambu, idan ya yi yawa ba ya jin mai. Amma, Allah Shi taimaki mai martaba, babban kuskure ne a bar samari matasa qatti kuma balagaggu suna sintiri, suna zarya a dukkan inda tashoshin mota da kasuwanni su ke, suna ta karakaina a cikin jama’a, su ba azumi suke yi ba, sannan kuma suna laluve ma jama’a aljifai, suna yi masu sata.
Allah Shi taimaki mai martaba, muna kira ga masarautar ka ta naxa kwamiti na fadawa ko dogarai, kowa a ba shi zabgegiyar bulala. Su rinqa kewayawa cikin birni su rinqa ba mutane waxanda ba su yin azumi kashi.
Ko jiya a daidai tashar KSTA a kan hanyar Batsari, da ido na Allah Ya nuna ma ni matasa, suna ta karakaina, kowannen su na riqe da taba sigari suna sha, ba kunya ba tsoron Allah, kuma suna masu yankan aljifan mutane. Ni kai na, sun xauke ma ni waya.
Bayan ni, sun xauke ma wani mutum tashi wayar ta kuxi kusan naira dubu talatin da takwas. Wannan fa rashin rowan sama, to sanadiyyar karya azumi ne da matasa ke yi.
Babban laifi kuma shi ne Hukuma ta na kallo ta sanya masu ido ba za ta iya xaukar mataki a kan suba. Wannan aiki, aikin masarautar Katsina ne, ko na ofishin Magajin garin Katsina, ba aikin gwamnan Katsina ba ne.
Idan ba a xauki mataki akan samari matasa da ba su yin azumi ba, to nan gaba ba mu san irin al’ummar da za mu riqa miqa ma Duniya ba.
Idan mutum ya san kurum ya tsugunna ya haihu amma bai san yanda za ya yi ya tarbiyyantar da xan ba, ya gwammace ya miqa ma Duniya ta ba shi tarbiyya, to haqqin masarauta ne ta tantance ta ladabtar da su ba don sun so ba.
A wani labari makamancin wannan kuma, a wasu qauyukan qananan hukumomin Batsari da Safana da Xanmusa, wasu varayin da aka yi sasanci da su, waxanda kuma yanzu su ne ke zuwa suna yi ma mutane hukunci da sata, ba ma dai garuruwan Babban Duhu (Safana) da Nahuta (Batsari) a cikin watan azumin nan, varayin na shigowa cikin jama’a suna zama cikin su, qiri-qiri suke cin abinci suna kuma shan taba sigari, da rana kata.
To idan ba su yin azumi, babu dalilin da za ya sanya su rinqa shigowa cikin jama’a bayin Allah suna yin ciye-ciye, suna kallon su. Yakamata gwamnati ta san wannan.
Wai, yau, sabili da lalacewa, an wayi gari, wai har wasu daga cikin varayin nan, fulani, har sun fara amsar kuxi a matsayin hukunci ko tara ga jama’a.
A cikin watan azumin nan, an yi haka ya kai sau uku a cikin qauyen Babban Duhu. Sun zo daga daji sun zo da niyyar kashe wani mutum a Babban Duhu, da jama’a suka lallashe su suka hana su, sai suka ce to sun qyale shi, amma sai ya biya kuxi naira dubu saba’in
(N70, 000). Dole sai da aka bi gida-gida aka tara masu kuxin aka ba su. Na biyu- wani yaron fulani ya zo yana kiwon shanu, sai aka duke shi.
Ya koma rugar su yana kuka. Sai suka yo zuga suka zo da bindigogi za su kashe mutane. Da aka ba su haquri, sai suka ce sun haqura amma a nemo wanda ya tava masu yaro. Aka bincika kaf qauyen Babban Duhu ba a gane wanda ya tava masu wannan yaro ba.
Ana ma tunanin wanda ya duke shi ba dan wannan qauyen ba ne. Amma duk da haka sai da suka nemi a ba su tsabar kuxi naira dubu xari shida (N600, 000) ko kuma su qona garin. Dole sai da aka tara masu kuxin aka ba su.
Na uku – sun zo qauyen suka tarar da wani mutum cikin mutane ana hira, suka ware shi za su daddatsa shi gunduwa-gunduwa. Mutane suka hana.
Wai suna zargin shi maye ne. Sai aka ce ma su ‘ai ya tuba’. Amma duk da haka said a suka sanya aka tara masu tsabar kuxi naira dubu arba’in (N40, 000).
Dukkan waxannan batutuwa uku Maigarin Babban Duhu ya faxa ma ni sub a wani ba daga wani wuri ballantana a ce labarum ba su da sahihanci.
Ba’ada bayan wannan, a cikin wannan watan na azumi kurum, a yankunan qananan hukumomin da aikin ta’addanci ya fi yawa, a jihar Katsina, kusan kullum sai varayi sun je sun kashe mutane aqalla daga xaya, kama abin da ya xara haka, su kuma raunata wasu.
Sai kuma sun gudu da wasu mutane, sannan su kwashe dabbobi. Yanzu ma, da suka ga babu matakin da hukuma ke xauka, a wasu
yankunan, da rana ko marece qiri-qiri suke zuwa suna fashi da makami.
Ko shekaranjiya da qarfe biyar na marece sun je qauyen Bakiyawa, sun kwashe kimanin awa biyu suna harbe-harbe, sun tattara shanu da sauran dabbobin gida.
A cikin azumin nan kawai, zuwan su Bakiyawa kusan na uku ken an. Ta kai ga, idan za su je qauye, wasiqa ma su ke aikawa su ce za su zo lokaci kaza, saboda lalacewa da tavarvarewar tsaro. Allah Ka zagaza ma na don iyyaka nah’budu. Ina tunanin, idan hukuma ba ta gaggauta xaukar mataki akan waxannan jahilan fulanin da Allah Ya tsine ma albarka ba, nan gaba kaxan za su fara ajiye tutocin su a waxannan yankuna da sunan sun fara gabatar da mulki ko hukunci kamar dai yanda ‘yan Boko Haram suka fara yi a wasu yankunan jihar Borno.
Saboda, ka san shi jahili ba ya da linzami. Babban linzamin sa shi ne gwamnati ta sa harsashi ta kau da shi daga doron qasa.
Amma hakan ya gagari gwamnatin. Allah Ya kawo mana qarshen waxannan mutane don alfalmar Annabi (SAW) da Alqur’ani mai tsarki. Allah Ka ceci bayinKa domin albarkacin wannan wata na alfarma.
Allah Ka yi ma shuwagabanni jagora, Ka taimaka ma su wajen sauke nauyin haqqoqin su akan jama’ar su. Muna fata mai martaba za ya taimaka, a cikin ayyukan sa na adalci ya duba wannan babbar matsala. Na gode. Dokta Aliyu Qanqara Ibrahim Ya Rubuto Ne Daga Cikin Birnin Katsina.
[covid-data]