Daga Sunusi Mailafiya
A cikin kasa da kwana uku bazan iya kididdiga adadin mutanen da sukai min korafi tare da neman sanin shin wai Shugaba Buhari ya san abubuwan dake faruwa a jihar sa ta haihuwa kuwa?
A Yadda yanzu mahara suka durfafi wasu yankuna da sace-sacen al’ummar yankin, da kuma kwashe dukiyoyinsu suyi awon gaba dasu, a yanzu har takai suna ji suna gani wannan maharan suke yi wa matayen su da yayansu fyade.
Bansan amsar da zan basu ba, domin ni dai ba’a fadar Villa nike ba, ballantana kai tsaye in amsa musu, babban abinda kawai na sani shi ne, Gwamnati tafi kowa kunnuwa da majiyoyi, idan har ma ace fadar Shugaban qasa batasan abinda ke faruwa cikin kwanakin nan ba, to ko tababa banayi cewar Gwamnatin jiha qarqashin Gwamna Masari tanada masaniya sarai akan wannan cin kashin kajin da ake musu.
Tun wasu lokuta da suka shude a baya na bawa Gwamnati shawara akan ta sanya dokar ta vaci akan harkar tsaro, musamman jihohin Katsina, Kaduna da kuma Zamfara.
Duk wani tunanin ka akan hanyoyin da za’a kawo qarshen ‘yan ta’adda a jihohin, baka kai tunanin Gwamnati wacce take da karfin jami’an tsaro da kayan fadan su ba, sun sani sarai cewar al’umma basu da wani qarfi wanda za su iya kare kawunansu, domin kare rayukan al’umma da dukiyoyin su wani ratayayyen nauyi ne akan Gwamnati.
Mu dauki al’amarin Boko haram mu ajjiyeshi a gefe, yanzu ba zaka iya qididdiga mutanen da masu garkuwa da mutane suka kashe a jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna da jihar Katsina ba, haka kuma ba zaka iya kissima adadin wanda fadan qabilanci a jihohin Filato da Kaduna ya kashe ba, duka kuma wasu mutane ne da suke rayuwa cikin al’umma, mutane ne da suke da maboyar da ansan inda za’a samesu, wannan shi ne banbancin yan Boko haram da masu garkuwa da mutane.
Yanzu bansan da wane irin kalami jam’iyyar APC mai mulki da mutanenta za su kwantar da hankulan mutanen jihar Katsinan ba, wanda cikin kwanaki uku zuwa huxu da suka shuxe mahara suka durfafi qarar da mutanen wasu yankuna, kullum cikin kuka da afi suke akan halin tausayawa da suke ciki, tare kuma da nuna gazawar Gwamnati wajen kare rayukan su.
Talakawan da suke rayuwa a birane da qauyuka, dukkan su suna da ilimin cewa haqqin Gwamnati ne ta kare rayukan su, sai gashi kuma suna ganin sabanin haka, sai gashi suna ganin tamkar Gwamnati ta manta cewar suna zaune ne a qasar ta, sai gashi suna kuka da hawayen su suna neman wanda zai tausaya musu, wanda zai tunkari waxannan mahara domin kare mutuncin su da rayukan su, to amma qemadagas daga vangaren jami’an tsaro.
Bazan gajiba, zan kuma jan hankalin Gwamnatin Tarayya data jiha akan al’amarin jihar Katsina, domin ya fara tuke al’umma, kuma haqurin mutane ya kusa kaiwa madakata akan irin salon gudummawar da Gwamnatin take bayarwa akan al’amarin wanda sam babu wani mafuta aciki.
A yanzu hankulan masu mulki ya koma kacokan kan cutar korona, wanda hakan yake zamar musu tamkar wani uziri da suke fakewa dashi, alhalin kuma gashi wasu mutane na amfani da wannan damar wajen yin awon gaba da mutane ba gaira ba dalili.
Tare kuma da neman makudan kuxaxe a matsayin fansa. Dole ne Gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin ta yi abinda shi ne ya kamaci Gwamnati. Samar da tsaro ba kamar yakin neman zave da tituna ko wuta bane, a’ah, kare rayukan mutane ne, domin ba wata qasa a duniya da zata more cigaban qasar ta idan har babu dawwamammen tsaro a kasar, mutanen da suke cikin ibtila’in rashin tsaron, sam yanzu ba ta wuta ko tituna suke ba, a gurin su wannan ba mahimmanci ne dashi kamar zaman lafiyar su ba, don haka dole ne Gwamnati ta dena wasa da rayukan al’umma tazo ta karesu. Lokacin da ake neman quri’unsu har kauyukansu da matsugunan su aka bisu da dadin baki, yanzu gashi an kasa shiga sako da lungu domin awon gaba da masu garkuwa dasu da kashe su. Ya kamata Gwamnati ta gane cewar lokacin wasa da hankulan talakawa ya zo qarshe fa.
Idan har Gwamnati kuma ta gaza wajen daqile wadannan yan ta’adda, ta bari suka ci gaba da cinikin rayukan al’umma, to na tabbata za ta ga fushin al’umar da take rainawa, na tabbata sai anzo lokacin da yan siyasa za su je yakin neman zave al’umma su rarakosu da takalman su a hannu, domin basuji qansu alokacin da suke buqatar tallafin Gwamnatin ba, kuma tabbas zasuyi fatali da duk wasu kayan zave da za’a aiko yankunan su da sunan zave, idan kuwa har haka tafara faruwa, to alamun juyin juya hali yana dab da faruwa a qasar da masu mulki suke ganin talakawa ba za su iya musu bore domin nemar wa kansu mafuta ba.